Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya mai girma sabon Gwamnan Jahar Zamfara, Alhaji Bello Matawallen Maradun! Ina fatan duk kuna cikin koshin lafiya kai da mukarraban ka? Allah yasa haka, amin.
Da fatan wannan sako nawa ya same ka cikin amincin Allah da rufin asirin sa? Allah yasa haka, amin.
Ina rokon Allah da ya baka mulki yayi maka jagora, yasa ka fara lafiya, kuma ka gama lafiya, amin.
Da farko ina mai kiran ka, kai da mukarraban ka, da kuji tsoron Allah mai girma da daukaka, sannan ku sani, shi mulki, Allah ne yake bayar da shi ga wanda yaso, kuma shine yake kwace shi daga hannun wanda yaso. Kuma ku sani, wannan abu da ya faru a Jahar mu ta Zamfara, iko ne na Allah, kuma Allah ne ya amsa addu’o’in talakawan Jahar Zamfara, ya dube su da idon rahama, ya karya masu lagon masu kama-karya, masu zaluntar su, ya kwace mulki daga hannun su ya baku! Kuma ku sani, yanzu talakawan Jahar Zamfara gaba dayan su idanuwan su suna gare ku, tare da tsammanin zaku taimaka masu, ko sa samu sa’ida ko sa samu canji daga halin da gwamnatin Abdul’aziz Yari ta saka su a ciki marar kyawo, halin kaka-ni-ka-yi, halin ni-‘ya-su!
Ya kai mai girma sabon Gwamna, ka sani, fahimtar cewa Allah ne ya karbe mulki daga hannun su ya baku domin ya jaraba ku, za ya taimaka maku matuka wurin sauke nauyin da Allah ya dora maku na al’ummar Jahar Zamfara. Sai ku zama masu tawali’u, masu sauraron talakawa, masu kishin al’ummah, masu tsoron Allah, masu tausayi da imani, masu girmama mutane, masu hakuri, masu kishin addini da gaske, masu girmama malamai, masu girmama sarakuna iyayen al’ummah, masu girmama ma’aikatan gwamnati, masu girmama ‘yan kasuwa, masu kishin ci gaban ilimi da dukkanin abun da zai kawo amfani da ci gaba da zaman lafiya da tsaro ga al’ummar Jahar Zamfara baki daya.

Ya kai Mai girma Alhaji Bello Matawallen Maradun, ka sani, kai da duk mukarraban ka, ya zama wajibi kuyi kokarin kauce wa irin hanyar da Abdul’aziz Yari da mukarraban sa suka bi, suka jefa Jahar Zamfara cikin matsalar da suka kasa fitar da ita. Ku zama masu zama cikin takakawan ku kuna sauraron matsalolin su da koke-koken su. Kar ka zama mai yiwa jama’ah girman kai da dagawa. Kar ka zama mai wulakanta jama’ah irin Abdul’aziz Yari. Ka sani, a halin yanzu amana ce Allah ya damka a hannun ka ta mulkin Zamfarawa baki daya, kuma ka sani Allah zai tambaye ka a kan wannan. Ka zama mai jin shawara, mai daukar shawarar manya. Kar ka yarda fadawan ka su zuga ka ka zama mai fada da jama’ah, domin su fadawa kawai suna neman abun sakawa aljihu ne, ba maslahar al’ummah ne a gaban su ba, ko maslahar ka kai kan ka!
Ya mai girma Matawallen Maradun, ka fi kowa sanin halin da Jahar mu take ciki na matsalar tsaro. Kayi kokari ka nemi taimakon Allah da shawarar wadanda ka san sun fika fahimtar abubuwa. Kar kayi wasa da addinin Allah, irin yadda Abdul’aziz Yari yayi. Kar kayi girman kai, ka nuna cewa kai ka san komai, ko ka nuna kai kafi kowa tun da kai ne Gwamna, don haka sai yadda kace za’ayi. Idan kayi haka, wallahi sai Allah ya cire hannun sa daga al’amarin ka, ya bar ka kayi maganin matsalolin ka da kan ka, ya ki taimakon ka, sai a wayi gari ka shiga matsala, kuma ka kasa sanin yadda zaka yi da matsalolin Jahar Zamfara, kamar yadda ya faru ga Abdul’aziz Yari.
Ina mai kara tunatar da kai da dukkan mukarraban ka cewa, ku sani, Allah ne yake bayar da mulki ga wanda yaso. An ruwaito daga Abdullahi Dan Abbas da Anas Dan Malik suka ce:
“A lokacin da Allah ya ba Annabi (SAW) nasara, suka ci Makkah da yaki, sai yayi wa al’ummar Musulmi bayani cewa, da yardar Allah yadda ya bamu nasara a kan Makkah haka zai bamu nasara a kan Farisa da Rum. Da jin haka sai munafukai daga cikin Musulmi da yahudawa suka fara surutu, suna ganin cewa wannan sam ba zai faru ba, har abada Muhammadu da mabiyansa ba za su samu karfin mulkin da har zasu mulki Farisa da Rum ba! Suka ci gaba da cewa, yaushe har wannan mutum Muhammadu ya gama da mulkin Makkah da Madinah har zai yi magana akan mulkin manyan dauloli irin Farisa da Rum? Shine sai Annabi (SAW) yace, ai Allah shine yake bayar da mulki ga wanda yaso, kuma ya kwace daga wanda yaso, don haka Allah zan roka ya damka mulkin wadannan manyan dauloli a karkashin Musulmi. Sai munafukan da yahudawan suka ci gaba da yin izgilanci da rashin kunya da ba’a ga Annabi (SAW), suna ganin cewa ai Annabi (SAW) bai isa ba. Kuma suna ganin cewa Farisa da Rum sun fi karfin sa, don haka Allah ba zai iya kwace mulki daga hannun su ya ba wa Musulmi ba. Shine sai Allah ya saukar da wannan aya, yana mai mayar da martani zuwa ga re su. Allah yace: “Kace (ya kai Muhammad), Ya Allah Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda kake so, kuma kana kwace mulki daga hannun wanda kake so, kuma kana daukaka wanda kake so, kuma kana kaskantar da wanda kake so, kuma dukkan alkhairi a hannun ka yake, kuma lallai kai mai iko ne akan komai.” [Suratu Ali Imran, 3:26]”
Ya ku bayin Allah! Lallai a cikin wannan aya mai girma akwai jan hankali da fadakarwa da tunatarwa da nuni akan godewa Allah madaukakin Sarki kan baiwa da ni’imah da yayi akan Manzon sa (SAW) da kuma wannan al’ummah. Domin Allah Subhanahu wa Ta’ala ya canza akalar Annabta da jagoranci da mulki da shugabanci daga hannun wadanda suke ganin sune isassu, in ba su ba babu wasu, wato bani Isra’ila, suna tunanin cewa tun da Allah ya basu mulki to baya iya kwacewa ya bai wa wasu. Musamman ma wadanda suka raina, suna ganin basu isa suyi mulki ba, wato Annabi (SAW), balarabe, bakuraishe, Dan Makkah, wanda ba ya rubutu ba ya karatu, wanda suke yiwa kallon Dan kauye, wanda bai waye ba, makiyayin dabbobi! Har suna cewa:
“Me yasa Allah bai saukar da Alkur’ani ko mulki ba akan wani (babban) mutum daga cikin manyan garuruwa biyu masu girma (wato Makkah da Ta’if)?” [Suratu Zukhruf, 31]
Shine sai Allah ya mayar masu da martani akan wannan magana ta su ta jahilci, yace:
“Shin sune suke raba rahamar Ubangijinka? Mu ne muke raba masu arzikinsu tsakaninsu anan duniya, kuma mu daukaka sashen su akan sashe da fifikon matsayi.” [Suratu Zukhruf, 32]
Kuma Allah ya sake fada cewa:
“Allah shine mafi sanin inda ya dace ya sanya Manzancin sa.” [Suratul An’am, 124]
Kuma Allah yace:
“Dubi yadda muka fifita sashen su akan sashe, kuma lahira ita ce tafi girman darajoji da girman falala.” [Suratul Isra’i, 21]
Ya kai mai girma Matawallen Maradun, ka sani, kai da dukkan mukarraban ka cewa, wadannan ayoyin Alkur’ani masu girma duk suna nuni ne da cewa, Allah ne yake bayar da mulki ga wanda yaso, don haka shine ya baku mulki domin ya gwada ku ya gani shin ku yaya za ku yi? Shin zaku zama masu kama-karya ne, masu dagawa da girman kai ga bayin sa, irin gwamnatin Abdul’aziz Yari ko kuwa zaku zama masu adalci, masu sauraro da tawali’u ga talakawan su? Shin zaku ci amanar Zamfarawa irin yadda Abdul’aziz Yari yaci amanar su, ko kuwa zaku rungumi talakawan ku? Toh, yanzu dai ga mulki nan Allah ya damka a hannun ku, kuma yana kallon ya ga shin yaya zaku yi? Don haka ya rage naku! Mu dai fatan mu da rokon Allah mu shine, Allah ya taimake ku, kuma yayi maku jagora, amin.
Idan kunyi da kyau, kun ji tsoron Allah, kun kamanta gaskiya, sai Allah ya sanya hannu a cikin mulkin ku, ya taimake ku, kuma ku gama lafiya, cikin mutunci, ana son ku ana kaunar ku. Kuma kuyi kyakkyawan karshe, ba irin karshen masu kama-karya ba. Amma idan aka samu akasin haka, to Allah zai mayar da ku ‘yan kallo, kamar yadda ya mayar da Abdul’aziz Yari da mukarraban sa ‘yan kallo a halin yanzu. Domin In Shaa Allahu ya gama siyasa a jihar Zamfara, kuma wallahi, abunda yayi wa Zamfarawa, sai Allah yayi masa fiye da haka. Sai ya ga sakamakon kama-karya da karfin Allah! Da ma ai mun sha fada masa, amma yayi biris, ya dauka wasa ne. Da yardar Allah sai ya zama abin misali, kuma sai yayi dana-sanin cin amanar Zamfarawa da yayi. Kuma abun da yake kokarin binnewa da yardar Allah sai Allah ya bayyana shi!
Daga karshe ina rokon Allah ya taimaki sabbin shugabannin Jahar Zamfara baki daya, ya taimaki shugabannin arewa baki daya da dukkanin shugabannin Najeriya baki-daya, amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku, Murtadha Muhammad Gusau, Babban limamin Masallacin Juma’ah na Nagazi-Uvete da Masallacin gidan Marigayi Alhaji Abdur-Rahman Okene, a garin Okene, Jahar Kogi, Najeriya. Za ku iya samun Liman ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.
Discussion about this post