Zamfara ta kirkiro sabbin masarautu

0

Majalisar dokoki ta jihjar Zamfara ta amince da kirkiro da masarautar Bazai daga masarautar Shinkafi.

Hakan ya biyo bayan neman majalisar tayi haka ne da mataimakin Kakakin Majalisar Abubakar Gumi ya mika a zauren majalisar.

Bayan bin neman ayi ba’asin hakan, majalisar ta amince da a kirkiro da Masarautar Bazai, sannan a daga darajar Hakimin Jangeru zuwa Sarki mai cin gashin kan sa da kuma Kayayen Mafara zuwa mukamin hakimi.

A yanzu dai Jihar Zamfara na da Manyan Masarautu 18 kenan a kananan hukumomi 14 da ke jihar.

Share.

game da Author