ZAMFARA: Haka Allah ya hukunta – Yari

0

Gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya bayyana cewa hukuncin Allah kwace jigar daga hannun APC da kotu tayi.

Yari ya ce ba zai ja da hukuncin Allah ba domin haka Allah yaso.

” Mun yi iya kokarin mu don ganin APC ce ta rike jam’iyyar APC ce ke mulki a jihar Zamfara, amma Allah bai sa haka ba. Mun yi tawakkali ga hukuncin Allah.

Idan ba a manta ba Kotun Koli ta soke kuri’un da aka kada wa jam’iyyar APC inda ta ce duk na banza ne domin ya tabbata basu ko yi zaben fidda gwani ba.

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa Bello Matawalle na jam’iyyar PDP ne zababben gwamnan jihar.

Shugaban hukumar Yakubu Mahmood ne ya sanar da haka a doguwar jawabi da yayi wa manema labarai a hukumar ranar Asabar, a Abuja.

Mahmood Yakubu ya ce bisa ga hukuncin da kotun koli ta yanke, Jam’iyyar PDP da ta zo na biyu a zaben ne za ta dare kan kujerun mulki a jihar.

Ta ce hukumar zata mika wa gwamna Bello Matawalle shaidar zama gwamna ranar Litinin.

Sabon Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle

1 – An haifi Bello Matawalle a garin Maradun ranar 12 ga watan Disamban 1969.

2 – Yayi makarantar Firamaren sa a garin Maradun a 1979.

3 – Daga nan sai ya garzaya Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Yaba dake Legas.

4 – Daga Ikko sai Matawalle ya nausa kasar Britaniya inda yayi karatun jami’ar sa a jami’ar Thames Valley University, London.

Aiki

1 – Matawalle ya fara aiki a ma’aikatar Lafiya a tsohuwar jihar Sokoto.

2 – Malamin makarantar Sakandaren mata dake garin Moriki da na garin Kwatarkwashi.

3 – Daga nan sai ya fara aiki a ma’aikatar albarkatun ruwa, Abuja.

Siyasa

1 – A 1998 Matawalle ya shiga harkar siyasa. Ya shiga jam’iyyar UNCP.

2 – Ya zama kwamishinan Kananan Hukumomi da masarautu, Kwamishinan raya karkara sannan kwamishinan matasa da wasanni daga 1999-2003.

3 – A watan Mayun 2003, an zabi Matawalle wakilin kananan hukumomin Bakura da Maradun a karkashin jam’iyyar ANPP zuwa majalisar Tarayya. Ya shugabanci kwamiti da dama a majalisar Tarayya har zuwa 2007.

4 – An sake zaben Matawalle a karo na biyu a 2007 sannan a 2009 da 2011 ya canja sheka zuwa jam’iyyar PDP inda aka zabe shi a karo na uku.

5 – Bello Matawalle ya zama zababben gwamnan jihar Zamfara ne bayan kotun Koli ta tabbatar da hukunci kotun daukaka kara ta yi cewa ba ta amince da ‘yan takaran jam’iyyar APC ba a zaben 2019.

6 – Kotun tace tabbas APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba. A dalilin haka ta kori duk wani dan takara na jam’iyyar APC tun daga kujerar majalisar jiha, Gwamna, Majalisar Tarayya da na Dattawa.

Share.

game da Author