Mazaunan karamar hukumar Birnin Magaji dake jihar Zamfara da wani soja sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa wasu mahara na shirin kawo farmaki a karamar hukumar.
Mazaunan sun bayyana cewa maharan na shirin yin haka ne domin daukan fansar kisan ‘yan uwan su guda bakwai da aka yi a Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin Magaji.
Wani mazaunin garin da baya so a fadi sunansa ya bayyana cewa sun ga dandazon mahara a bayan garin suna shirya yadda za su far wa garin Birnin Magajin.
Ya ce matasan garin suma suna zauna ne a shiri sannan wasu da dama daga kauyukan dake kusa dasu duk sun taho domin taya su tsare garin.
Karamar Hukumar Dan Magaji dai ita ce Karamar hukumar Ministan tsaro na kasa Mansur Dan-Ali.
Kakakin rundunar ‘Operation Sharan daji’ Clement Abiade ya tabbatar da haka sannan ya ce suma sun nemi akawo musu karin Sojoji domin kwana cikin shiri.
Idan ba a manta ba a safiyan yau Alhamis ne dandazaon mafusata suka yi wa Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin Magaji kawanya, suka kashe wasu da ake zargi mahara ne har su bakwai.
An ce wadannan mahara sun je Fadar Dan Alin Birnin Magaji ne domin tattauna batun sasantawa, bayan kwace musu shanu da aka yi, sakamakon harin da aka ce an kai musu ta sojojin sama a dajin Birnin Magaji.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa bayan harin da aka kai Dajin Birnin Magaji a ranar 4 Ga Afrilu, sai mazauna yankunan suka raka sojoji har cikin dajin, inda aka samu shanu sama da 200 da aka sace.
An ajiye shanun a fadar Dan Alin Birnin Magaji, sai dai kuma cikin makon da ya gabata ne aka kwashe shanun zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Yayin da jama’ar gari suka ji labarin taron da ake yi a fadar sarki, sai suka garzaya suka yi wa fadar kawanya, har suka yi yunkurin banka mata wuta.
Sai dai kuma an ce sojojin da ke gadin fadar sun ba da hakuri, ba a banka mata wutar ba.