ZABEN 2019: Jam’iyyu 75 sun yaba wa Shugaban INEC

0

Jam’iyyu 75 sun jinjina wa kokarin Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.

Cikin takardar bayan taro da suka fitar jiya Litinun a Abuja, jam’iyyun sun amince tare da gamsuwa da cewa Yakubu da INEC sun yi rawar gani matuka wajen gudanar da zaben 2019.

Taron wanda Kungiyar CAT da jam’iyyu 75 suka shirya shi domin bin bitar yadda zaben 2019 ya gudana, sun amince da cewa yawancin matsalolin da aka fuskanta, duk ba laifin INEC ba ne.

Sun ce sai da yawa INEC ta sha sanar da cewa a kiyaye aiwatar da wasu laifuka a lokacin zabe, amma da dama wasu suka yi kunnen-uwar-shegu da umarnin na INEC.

Dangane da haka, sun fitar da takardar jinjina tare da yabawa ga Shugaban INEC da kuma ita kan ta INEC din.

Sun yi kira ga INEC ta karfafa ma’aikatan ta, ta hanyar kara yi masu horo, musamman a kan aiki da na’urar Card Reader.

Sun yi kira ga Majalisar Tarayya da ta sake gaggauta aika wa Shugaba Mujammadu Buhari Kudirin Gyaran Dokokin Zabe domin a tabbatar da an maida su doka.

Jam’iyyun 75 sun ni a gaggauta kafa Kotunan Musamman Na Hukunta Masu Laifukan Zabe.

Sun ce a kafa kotunan wata daya kacal bayan kammala shari’un kararraki zabe da ake kan yi a yanzu.

Ka kara yawan jami’an tsaro a runfunan zabe a lokutan zabe

Sum kuma yi kira a fito da tsarin zabe na bai-daya, yadda hakan kashe kudade da kuma cusa wa jama’a kishin fitowa su zabi jagorori nagari.

Jam’iyyun siyasa su kimtsa kan su tare da sake saisaita tsarin tafiyar da jam’iyya.

Jam’iyyu su kawar da rigingimu a lokutan zaben-fidda-gwani. Idan sun yi haka, zai taimaka wajen ganin zabe ya kara samun nasarar gudanarwa sosai da sosai.

Cikin jam’iyyun da suka halarci taron, har akwai LP, PPA, A. NCP da sauran su.

Mataimakin Daraktan CTA, Faith Nwadishi da Shugaban C4C, Geff Ojinike ne suka sa wa takardar hannu a madadin sauran jam’iyyu.

Share.

game da Author