Za a fara yi wa Fulani makiyaya rajistar dole a Jihar Ekiti

0

Gwamnatin Jihar Ekiti ta bayyana cewa za ta fara yi wa Fulani makiyaya rajista domin yin hakan zai kara samar da tsaron kare lafiya, dukiya da rayukan ‘yan jihar.

Gwamnatin ta ce idan aka yi musu rajista, hakan zai kara nesata rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma, wanda kan faru idan shanu sun ci amfani gonar wani manomi.

Babban Jami’in Hukumar Hana Kiwo Barkatai a Jihar Ekiti, Sola Durodola ne ya bayyana haka ga manema labarai a Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Ya kara da cewa yin hakan ya zama wajibi, domin aniyar gwamnatin wajen ganin an kauce wa fadace-fadace tsakanin makiyaya da manoma a fadin jihar.

Durodola ya ce idan aka yi wa Fulanin rajista, zai taimaka wajen zakulo duk inda wani yay i wa mai gona barna, ko kuma ya aikata babban laifi a duk ma inda ya ke a cikin jihar Ekiti.

An bukaci Fulani makiyaya su cika fam, inda kowa zai bayyana inda ya ke, daga nan gwamnati za ta bai wa kowanen su lambar rajistar sa wadda ke nuna ko shi wane ne kuma inda ya ke zaune.

“Ba za mu yarda haka kawai Fulani makiyaya su rika kashe mana jama’a ba, su na lalata musu amfanin gona da sunan wai su na kiwo.” Inji Durodala.

Gwamnatin tsohon gwamna, Ayo Fayose ce ta fara shigo da batun yi wa makiyaya rajsita a jihar.

Sai dai kuma an tsaida shirin bayan da ya rika samun suka, inda wasu ke cewa adawar siyasa ce kawai don Fayose ya na PDP.

Yanzu kuma APC ta hau gwamnati a jihar, za ta fara yi wa makiyaya rajista, saboda alfanun abin da ta ce ta hango.

Share.

game da Author