Ministan Kudi Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnati za ta fara biyan masu yi wa kasa hidima (NYSC) da sabon tsarin mafi kankantar albashi wato naira 30,000.
Jaridar ‘ The Nation’ ne ya wallafa wannan albishir daga minista Zainab zuwa ga masu bautar kasa.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya tsohon shugaban hukumar NYSC Suleiman Kazaure ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai gwamnati zata fara biyan masu aikin yi wa kasa hidima Naira 31,800.
” A 2011 ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kara alawus din masu aikin yi wa kasa hidima daga Naira 7,800 zuwa 91,800 sannan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a sabon tsarin albashi gwamnati ta yarda ta fara biyan su Naira 30,000.
Zainab ta ce duk da haka gwamnati na nan na tattaunawa da kungiyoyin kwadago domin gano hanyar da ya fi dacewa abi don fara aiwatar da sabon albashi da tuni ya zama doka a kasa.