‘Yan Najeriya sun fito a shafukan sada zumunta a yanar gizo, musamman a tiwita, su na caccakar Shugaba Muhammadu Buhari, dangane da wani barkwanci da ya yi a kan matsalar tsaro a Najeriya.
Ranar Lahadi ne Buhari ya yi wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda barkwanci cewa ya ga duk ya rame, ya rage kiba, saboda matsalar tsaro a kasar nan.
Wani bidiyo da ake ta watsawa, an nuno Shugaba Buhari na hira da manema labarai bayan dawowar sa.
An yi masa tambaya dangane da matsalar tsaro a fadin kasar nan, musamman yawaitar garkuwa sa mutane.
Buhari ya amsa da cewa, “babu wata hanyar da za a yi tunanin samu da ta fi wadda ake a kai yanzu wajen magance matsalar tsaro.”
Ya kuma kara da cewa, “Ai na ga har Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya rage kiba, saboda fuskantar kalubalen tsaro a kasar nan.’
Nan da nan wadanda wannan barkwanci bai yi wa dadi ba, suka fara caccakar Shugaba Muhammadu Buhari a shafukan su na tweeter.
Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin AAC, Sowore, ya rubuta cewa, ” Buhari fa ya saki layi. Wannan babbar katobara ce.”
Obey Ezekwesili kuwa cewa ta yi, “yanzu kisan jama’a shi ne zai zama abin barkwanci kuma? Wannan kamar wanka ne da jinainan jama’ar da ake kashewa.
“Kai ne Babban Kwamandan Askarawan Kasar nan. Amma wata rana ‘yan Najeriya za su kawo karshen wannan barkwancin.”
Wasu da dama sun rika rubuta kakkausan kalamai a shafukan na su na tiwita.
Discussion about this post