Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa wasu tsirarun ’yan siyasar da suka fadi zabe ne ke da hannu wajen ruruta wutar rashin tsaro a kwasu yankuna na kasar nan.
Buratai ya yi wannan furuci ne jiya Laraba a Maiduguri, babban birnin jihar Barno, a lokacin da ya karbi bakuncin Kwamitin Majalisar Tarayya na Sojoji, a karkashin jagorancin shugaban Kwamitin, Remande Shawulu a Cibiyar Tsare-tsaren Farmaki a Maiduguri.
Laftanar Janar Buratai, ya ce “Irin dimbin kalubalen tsaron da ake fuskanta yanzu a kasar nan, a Arewa ta maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da ma wasu sassan kasar nan, na yi amanna da cewa su na faruwa ne sakamakon yadda zaben 2019 bai yi wa wasu dadi ba.
“Akwai sa hannun ‘yan siyasa a cikin kalubalen sosai. Wadanda zabe bai yi musu dadi ba, su na kokarin daukar fansa ko huce haushi ta hanyar daukar nauyin masu tayar da fitintinu.
“Abin akwai siyasa sosai a ciki. Kuma siyasar ta yi katutu a cikin matsalar tsaron.
“Don haka ina so na yi amfani da wannan daman a yi kira ga ‘Yan Majalisar Tarayya, su ja hankalin wadannan ‘yan siyasa da su sa kaunar kasar su kafin burukan su na siyasa.
“Mu na da hujjoji masu karfi, amma kawai dai mu na taka-tsantsan don kada mu fallasa abin da ba hakan ya ke ba.” Inji Buratai
Shawulu ya ce kwamitin sa sun kai ziyarar ce domin ganin irin ci gaban da aka samu a fannin tsaro a Arewa maso Gaban.