Yadda zamu yi rabon kudin tallafi na BHCPF – NHIS

0

Hukumar inshoran kiwon lafiya ta kasa (NHIS) ta bayyana cewa ta samu naira biliyan 6.5 a kudin tallafin na Basic Health Care Provision Fund (BHCPF) zuwa yanzu.

Jami’in hukumar Uchenna Ewelike ya sanar da haka a taro a Abuja.

Ewelike ya bayyana cewa NHIS ta raba Naira biliyan 12.7 wa jihohin da suka cika sharuddan samun wannan tallafi.

Ya kuma bayyana hanyoyin da hukumar ta tsara domin rabon wannan kudade.

YADDA NHIS ZA TA RABA TALLAFIN BHCPF

Ewelike yace idan ba a manta ba a shekarar 2018 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince gwamnati ta ware kashi daya daga cikin kasafin kudaden ta na duk shekara domin ingata kiwon lafiya.

A lissafe adadin yawan kudaden sun kai biliyan 55 sannan a yanzu haka NHIS ta samu kashi 25 bisa 100 na kudaden.

Ewelike yace hukumar ta amince ta baiwa hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) kashi 45 na kudaden domin tabbatar cewa mutane musamman mazauna karkara sun mori lagwadan wannan tallafi.

Kashi biyar bisa 100 na kudaden zai shiga asusun hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) domin aikin hana yaduwar cututtuka.

Sannan NHIS zata yi amfani da kashi 50 bisa 100.

Idan ba a manta ba Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa har yanzu akwai jihohi 14 a kasar nan da basu karbi kudin tallafin kiwon lafiya na ‘Basic Health Care Provision Fund (BHCPF)’ ba.

Adewole ya fadi haka a zauren majalisar dattawa inda ya kara da cewa jihohi 22 ne suke karban wannan tallafi.

Ya ce rashin nuna ra’ayin karban tallafin da rashin cika sharuddan samun tallafin na daga cikin dalilan da ya hana wadannan jihohin samun tallafin.

” Sharuddan samun tallafin sun hada da kafa hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, Kafa inshoran kiwon lafiya na jihar da bada gudunmawar Naira biliyan 100.

Ga jerin jihohin

1. Kebbi

2. Jigawa

3. Akwa Ibom

4. Cross River

5. Gombe

6. Rivers

7. Borno

8. Zamfara.

9. Ondo

10. Benue

11. Taraba

12. Nasarawa

13. Ogun

14. Sokoto.

Korafin wasu ma’aikatan kiwon lafiya game da tallafin BHCPF

Wasu ma’aikatan kiwon lafiya sun koka cewa kashi 25 bisa 100 da gwamnati ta bada ba za su isa warware matsalolin da fannin kiwon lafiyar kasar nan ke fama da su ba.

Shugaban kungiyar rajin kare fannin kiwon lafiya Oladipo Ladipo ya bayyana haka.

Share.

game da Author