Dandazaon mafusata sun yi wa Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin Magaji kawanya, suka kashe wasu da ake zargi mahara ne har su bakwai.
An ce wadannan mahara sun je Fadar Dan Alin Birnin Magaji ne domin tattauna batun sasantawa, bayan kwace musu shanu da aka yi, sakamakon harin da aka ce an kai musu ta sojojin sama a dajin Birnin Magaji.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa bayan harin da aka kai Dajin Birnin Magaji a ranar 4 Ga Afrilu, sai mazauna yankunan suka raka sojoji har cikin dajin, inda aka samu shanu sama da 200 da aka sace.
An ajiye shanun a fadar Dan Alin Birnin Magaji, sai dai kuma cikin makon da ya gabata ne aka kwashe shanun zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Bayanai sun tabbatar da cewa ranar Laraba sai ga wasu mutane bakwai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da wani shi ma da ake zargin jami’in SSS ne, suka je fadar sarki.
An ce sun je ne domin su roki alfarmar a saki shanun. Haka dai wani dan garin ya shaida wa wakilin mu, tare da neman afuwar kada a bayyana sunan sa.
An ce a lokacin Sarkin Birnin Magaji ya na Kaduna, ba ya gari a lokacin da suka isa.
Sai Sakataren sa Muhammadu Mai-Inji, ya sauke su a cikin fada.
Yayin da jama’ar gari suka ji labarin taron da ake yi a fadar sarki, sai suka garzaya suka yi wa fadar kawanya, har suka yi yunkurin banka mata wuta.
Sai dai kuma an ce sojojin da ke gadin fadar sun ba da hakuri, ba a banka mata wutar ba.
Su kuma jama’ar gari ashe ba su hakura ba, suka yi tsaye har sai da wadannan mahara suka fito daga cikin fada. Nan take suka rufe su da dukan tsiya, suka yi musu kisan-rubdugu nan take, sannan kuma suka kone motar jami’an SSS wadda aka dauko su a ciki.
Duk da shi ma jami’in SSS da ke tare da su ya ci dukan tsiya, bai mutu ba, domin sojoji sun cece shi da kyar. Sai dai kuma an ji masa mumunan raunuka.
Jami’an ’yan sandan Zamfara dai har yau ba su ce komai ba a kan batun. Shi ma kakakin su Mohammed Shehu an kira wayar sa, amma bai amsa ba.