Najeriya ta afka cikin matsalar hasken wutar lantarkin da ba ta taba fadawa ba, sakamakon lalacewar injinan rarraba hasken lantarki a Cibiyar Tattarawa Da Rarraba Wuta ta Kasa.
Lamarin ya faru tun a ranar Laraba, inda kusan gaba dayan kasar nan ya fada cikin matsalar rashin hasken lantarki.
Wannan matsala ta bijiro a daidai lokacin da Arewacin Najeriya, musamman Sakkwato, Katsina da Maiduguri ke kukan zafin rana ya haura digiri 42 na ma’aunin zafin rana.
Daga ranar Laraba har zuwa jiya Alhamis, sai da karfin miga watts na wutar lantarki ya durkushe zuwa 280, maimakon 4,032 har ranar Talata, kwana daya kafin Laraba.
Wasu injiniyoyi biyu sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa, ko da za a iya shawo kan matsalar, to sai an shafe kwanaki uku.
Daga Laraba har zuwa yau wayewar garin Juma’a, ana tsakurar wutar a ba wasu jihohin, wasu kuma ko kyalla musu ta minti daya ba a yi.
Jihohin Keffi, Nasarawa, Neja da Babban Birnin Tarayya Abuja, sun samu miga watts 20 kacal daga Kamfanin Raba Lantarki na AEDC, a ranar Laraba da safe. Can zuwa yamma kuma aka kara musu zuwa miga watts 70, duk kuwa da cewa mutanen yankin sun haura milyan 13.
Kamfanin Raba Lantarki na Yola, YEDC, bai samu raba ko miga watts daya kacal a jihohin Arewa maso Gabas ba.
Kakakin Kamfanin TCN ya ki daukar waya domin ya yi wa PREMIUM TIMES karin bayani.
Idan ba a manta ba, cikin watan Mayu, 2016, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin samar da miga watts 10,000 a zangon sa ba farko.
Rabon da a samu irin wannan matsalar tun cikin 2018. Ko wadda aka samu a 2013 ba ta kai munin ta wannan lokacin da mu ke ciki ba.