Yadda Ganduje ragargaza dadadden tarihin masarautar Kano cikin kwana uku

0

Kirkiro da sabbin masarautu da gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi a makon da ya gaba ya wuce ace wai kawai yana daukar fansa ko kuma don ya tozarta sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne, abin da yayi ya ragargaza dadadden tarihin masarautar Kano da ta yi suna matuka a tarihin masarautun Najeriya ne.

Kafin daddatsa masarautar Kano da gwamna Ganduje yayi jihar Kano na daure tamau ne a matsayin masarauta daya mai cin gashin kanta baya ga kirkiro masarautar Sarkin musulmi a Sokoto a 1804.

Ganduje yace ba bibiyan Sarki Sanusi yake yi ba kirkiro sabbin masarautu da yayi. Hasali ma yace ai shi ya fi karfin kujerar Sanusi din domin da shugaban karamar hukuma ya kamata yana gugan sahu kamar yadda dokar Najeriya ya gindaya.

A fili yake cewa Ganduje basu ga maciji da Sarki Sanusi. Ko ma an hadu, na ciki na ciki ne.

Tun a 2017 ne a ka rika zuga gwamna Ganduje da ya tsige sarki Sanusi bisa zargin wai an samu matsala a asusun masarautan jihar.

” Gyara ne da ci gaba muka kawo jihar mu. Muna so mu kusanto da mutane kusa da shugabannin su. Amma ba daukar fansa ba ko kuma bibiyar wani.

” Idan ma har zancen ake so a yi ay a karkashin shugaban karamar hukuma ya ke ba gwamna ba.

” Idan ba dun-ba-dun ba, ay da shugaban hukuma ya kamata yake gani idan bukatan haka ya tashi ba gwamna ba domin gwamna ya yi masa nisa. Haka dokar kasa ta gindaya.

” Wannan masarautu da muka kirkiro za mu tabbata mun gyara su sannan mun daga darajarsu da martaba a Idanun mutanen jihar.

Ganduje ya ce mutanen jihar na murna da wannan ma

Umarni Kotu:

Duk da umarnin da kotu ta bada cewa gwamnatin Kano ta dakatar da kirkiro sabbin masarautu a Kano, gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya nada sabbin sarakunan wadannan masarautu.

Ganduje ya ce ya riga ya nada sabbin sarakunan kafin hukuncin da kotu ta yanke na dakatar da shi.

Wadanda Ganduje ya nada kuwa sun hada

Ibrahim Abubakar II, Sarkin Karaye, Tafida Abubakar Il, sarkin Rano, Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi, Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya.

Idan ba a manta ba Babbar Kotun Jihar Kano ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje nada masarautu, har sai ta saurari karar da Gungun Mambobin Majalisar Dokokin Jihar ’yan jam’iyyar PDP suka kai gaban ta.

Majalisar Kano

A ranar Juma’a ne mabobin jam’iyyar PDP a Majalisar Dokoki ta Jihar Kano suka garzaya kotu domin su hana Ganduje nadawa da kuma rantsar da sarakunan da ya nada a masarautu hudu da ya kara kafawa a lokacin da ya sa dokar daddatsa masarautar Kano.

Mambobin wadanda su ne marasa rinjaye, sun shigar da karar ca a bisa jagorancin Shugaban Masara Rinjaye, Rabiu Gwarzo, sun garzaya kotun domin neman a dakatar da Ganduje daga rantsar da nada sabbin sarakunan da ya yi niyyar yi a yau Juma’a, a bisa wasu dalilai biyar.

Sun bayyana wa kotu cewa ba a bi ka’idar da ya kamata a kira taron zama a zauren majalisa ba, kafin majalisa ta zartas da dokar karin masarautun guda hudu.

An yi zaman cikin gaggawa, kuma Gwamna Ganduje ya sa wa dokar hannu cikin gaggawa. Sannan kuma yay i gaggawar nada sakakunan, duk a cikin kwanaki biyu.

Sannan kuma a ranar ne Juma’a Ganduje ya shirya zai rantsar da su, kafin a shigar da karar taka masa burki.

Mai Shari’a Nasiru Saminu ya dakatar da Ganduje daga kirkiro Masrautun Gwarzo, Rano, Bichi da kuma Gaya.

Dawowar Sarki Sanusi

A yau Lahadi ne ake sauraron saukar jirgin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a filin jirgin Aminu kano bayan tafiya da yayi kasar Ingila.

Dubban magoya bayan sarki Sanusi da mutanen Kano ne suka yi tattaki zuwa filin jirgin saman domin jiran saukan jirgin sarki Sanusi.

Wasu da suka zanta da wakilin mu a Kano sun ce garin ya rincabe, masoyan sarki Sanusi sun fito kwansu da kwarkwata domin yi wa sarkin Lale-marhaban.

Ana sa ran jirgin Sarki zai sauka ne da misalin Karfe 4 na yamma a filin jirgi na Aminu Kano.

Har yanzu dai sarkin Kano Sanusi bai ce uffan ba game da daddatsa masarautar Kano da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje yayi.

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya fasa masarautar Kano inda ya kirkiro sabbin masarautu har guda hudu.

Mutane da dama sun yi tir da wannan masarautu da Ganduje ya kirkiru suna masu cewa yana yi wa sarki bita da kulli ne kawai don siyasa ba wai don yaga hakan ya cancanta a yi ba ko kuma daukakar jihar Kano.

Cikin kwana uku kacal, majalisar jihar Kano karanta wannan kudiri da wani dan majalisa ya mika a gabanta. A rana ta karshe kuwa wato cikon na ukun, Kakakin Majalisa da wasu daga cikin wakilan majalisar suka garzaya fadar gwamnati inda nan take gwamna Ganduje bai yi wata-wata ba rattaba hannau a wannan kudiri ta zama doka.

Ba mu ba Gaya, muna tare da Kano ne – Mutanen Wudil

Mutanen karamar hukumar Wudil dake jihar Kano sun yi kira da kakkausar murya ga gwamnatin jihar Kano da ta sani cewa ba za ta hade da masarautar Gaya ba kamar yadda ya nuna a sabbin masarautun ga aka kirkiro.

Shugaban kungiyar, Yawale Idris ya sanar da haka a taron ‘yan jarida a Kano.

” Babu wanda ya tuntube mu kafin a aiwatar da wannan sabon abu. Mu mutanen Wudil ba tare muke da Gaya ba, saboda haka dole a koma kan teburin shawara a maido da yadda tsarin yake tuntuni domin ba zamu yarda a sakalamu a wani masarauta da bamu da alaka ko tarihi da su ba.

Idris yace tabbas ida har aka yi haka to kiri-kiri ana shafe tarihin su ne a doron kasa.

” Muna da asalin mu kuma muna da cikakken tarihin mutanen mu. Mu Jobawa ne wanda daya ne daga cikin gidajen sarautar Kano da ke da Tuta saboda haka muna so gwamnan Kano ya sani. Sannan kuma muna so ya sani cewa dukkan mutanen Mudil mun yi mubaya a ne ga sarkin Kano Sanusi da masarautar Kano ba za mu bi masarautar Gaya ba.

” Tun a lokacin jihadin Usman Danfodio gidajen fulani biyar ne aka basu tuta a Kano wadanna gidaje kuwa sune, Sullubawa (wanda shine gidan su Sarki Sanusi mai mulki), Jobawa ( Masu sarautar Wudil), Yolawa (Masu sarautar Dawakin Tofa), Danbazawa (Masu sarautar Dambatta) da Gyanawa ( Masu sarautar Gabasawa).

Share.

game da Author