Yadda Buhari ya shafe shekaru hudu ya na karya ka’idojin bayar da kwangiloli

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabannin da aka yi kafin shi, inda ya shafe shekaru hudu ya na mulki, ba tare da kafa Hukumar Kula da Ka’idojin Kwangilolin Gwamnati ba.

Buhari wanda ya shafe shekaru 12 ya na fafutikar neman zama shugaban kasa, ya rika jaddada cewa zai yi aiki kamar yadda dokar kasa ta tanadar, wato ‘rule of law.’

Dokar Najeriya wadda ta samar da Dokar Bada Kwangiloli ta 2007, ta shar’anta cewa wajibin shugaban kasa ne ya kafa Hukumar Kula da Ka’idojin Bada Kwangiloli, da a Turance ake kira ‘National Council for Public Procurement’.

Sannan kuma wannan hukuma ita ce za ta rika kula da hukumar BPP, wanda ke yanka wa kayan gwamnati farashi da kuma saida kadarorin gwamnati.

Sai dai kuma duk da alkawurran da Buhari ya sha yi cewa zai kafa hukumar, har ya kammala zangon sa na farko a yau Laraba, bai kafa hukumar ba.

Wannan ce ta sa Majalisar Zartaswa ta handame karfin ikon hukumar a wannan zango na Buhari na farko, ta rika bayar da kwangilolin da kan ta.

Kamar yadda Buhari ya yi, haka shi ma marigayi Umaru Musa da Goodluck Jonathan suka rika yi.

Kafin Buhari ya hau mulki, ya rika yin alkawarin cewa ba zai yi duk wani abu da shugabannin da suka yi kafin shi ba suka rika yi, matsawar doka ba ta ce ya yi ba.

‘Yar’Adua ne ya saw a dokar hannu a ranar 4 Ga Yuni, 2007. Sai dai kuma har ya rasu bai yi aiki da ita ba.

Share.

game da Author