Abubuwa da dama da duniya take kunshe da su dole a lokuta mabambanta su farantawa mutum ko akasin haka. Hakanan abubuwan da suke kunshe a lahira ma, dole ne wasu su yi murna da shi ko shima akasin haka.
Tarihi dai na duniya ya biyo ta fuskar jagoranci, kuma jagoranci ta fuskar ilimi da sanin wani abu da wasu basu sani ba. Akan wannan sharadi ne, har Annabi Adamu ya zama mafifici a cikin sauran halittun da Ubangiji Ya halitta. Wanda saboda girman kai Shaidan ya bijirewa umarnin yi masa biyayya har aka la’anceshi kamar yanda Qur’ani mai tsarki ya shaida mana.
To tun daga wancan lokaci, masana ilimi sune ke jagorantar al’umma. A sannu a hankali duniya na tafiya, dubunnan shekaru na shudewa har ta kai matsayin masu son zuciya sun fara kawar da tasirin Malamai ko masana a bangarorin addinai na wancan zamanai.
Dabarar da suka yi sai su karbe mulkin, sai kuma su janyo masana su nadasu kusa da su. Wadannan masana su kan futo daga bangaren addinin Allah ko kiristanci ko maguzanci. A haka dai ake ta ci gaba da tafiya.

Dubannan shekaru na karuwa, wayewa na shigar mutane, har aka kai matsayin dai Jarumi ne kadai zai iya zama Sarki ko Jagoran wata daula ko masarauta. Wannan jarumta ta kan samo asali ko dai ta fuskar addini, wato ace malami ne da yake a addu’oi, ko kuma ta fuskar maguzanci da ake amfani da tsafi da bori don mulkar mutane. Wannan yanayi ya jima yana haifar da shugabanni a duniya, har zuwa karni na wajen 18 da su Dan fodio suka yi jihadi don tabbatar da mulkin muslunci kamar yanda shari’ah ta gindaya.
Wannan shine babban matakin da aka fara bi don rusa mulkin maguzanci, aka mayar da shi na addini zallah. A takaice, a wancan lokaci, Sarakunan Hausawa akan kira su da Habe, su ne wadanda su Bagauda da zuri’arsa suka yi mulki a kasar Kano, tare da maye gurbinsu da sarakunan Fulani, wanda al’ummar Kano suka amince da Sulaiman b. Aba Hama, bayan shi Sheikh Muhammad Bello ya umarcesu da su zabi jagoransu a Birnin Gada a wajejen shekarar 1221 bayan hijira, daidai da watan Fabarairu da Maris na shekarar 1806 miladiyya.
Bayan Sarki Sulaiman ya rasu ranar 22 ga watan Ogustar 1819, sai aka nada Ibrahim Dabo a matsayin sabon Amir na Kano bayan ya samu sahalewa daga sarkin musulmi Muhammadu Bello a ranar 21 ga watan Satumbar 1819.
Da yake akan rikicin da ya taso akan masarautar Kano nake so magana, shi yake na kwaso wannan mabudi don yin magana sosai akan jikokin Dabon baki daya.
Shekaru da dama bayan sun yi nisa, an sha fama da rikicin cikin gida akan zuri’ar gidan Dabo. Abubuwa ba su fara dagule musu ba, sai bayan shigowar turawan mulkin mallaka. Daganan ne matsaloli marasa dadi suke ta faruwa daya bayan daya, saboda rage musu iko da karfi da turawa suka yi.
Sarkin Muhammad Abbas shine sarkin Kano na farko bayan turawa sun kifar da mulkin muslunci na su Danfodio a 1903. A haka yau fari gobe tsumma ake ta mulki, aka mayar da sarakuna tamkar dillalai akan jama’arsu. Su samu mutane su yi musu bayani, sai kuma su koma wajen Turawa su basu amsa. Wannan mulki mara kyan fasali shi ya kawomu har aka bayar da ‘yancin kai a 1960. Duk da cewar turawan sun tafi, to amma darajar sarakunan fulani ta tafi, illa kadan da aka bari. Wacce ta kunshi karbar kudin haraji da su hukunci da sauransu, amma dole sai da amincewar Premier, mu anan Arewa shine Sir. Ahmadu Bello.
Kuskure na farko ko targade da aka yi wa masarautar Kano shine, sabanin da aka samu a jam’iyyar NPC tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Sunusi I da kuma firimiya Amadu Bello. Wanda yanayi ne ya sa har aka yi amfani da karfin ikon gwamnati aka tsige Sarkin daga kan mulki a watan Afrilun shekarar 1963. Wannan abu da aka yi, shi ya bayar da damar Gwamnan Kano Abubakar Rimi shi ma ya keta masarautar Kano karkashin mulkin Ado Bayero, a zangon Rimin na farko a 1979.
Rimi ya samu damar fasa Kano zuwa masarautu biyar kamar haka; Rano, Gaya, Karaye, Dutse da kuma Auyo.
Sai dai bayan an yi amfani da siyasa, har Rimi ya kasa zarcewa akan kujerar gwamna, a karshe Sabo Bakin Zuwo ya zama gwamna, ya yi amfani da ikonsa, ya rushe wadancan masarautu kamar yanda ya samar a filin sukuwa lokacin suna tare da Ado Bayero a shekarar 1983. In da har yayi wani barkwanci yace an kawar da Sarakunan Caka, Dusa da Kubuja. Ake ta sowa!
Wani abin nazari akan wannan abubuwa biyu da suka faru na Sardauna da Rimi, Sarkin Musulmi na lokacin da aka yi duk abubuwa biyun akan idanunsa wato Sultan Siddiq Abubakar III, bai dauki wani mataki mai tsauri don kare martabar Sarakunan ba. Wata kila shima yana fargabar rasa rawaninsa ne.
A watannan na Mayu, 2019, Gwamna Ganduje shima ya aikata hakan na rarraba masarautar Kano zuwa biyar dalilin siyasa kai tsaye.
Magana ta farko Sarki Sunusi II yana da kaifin baki da rashin rufe baki idan ana aikata ba daidai ba. Kuma ko ba komai yana da saurin daukar layi akan duk wani abu da yayi amanna da shi. Akan hakane ya bi bayan dan takarar gwamnan Kano na PDP, Engr. Abba K Yusuf, wanda hakan ya batawa Ganduje rai sosai.
Kuma abu na gaba, Sarki ya samu yardar Kwankwaso ne har ya zama Sarki. Kuma duk wata kujera da Sanata Kwankwaso ya nada a baya, Ganduje ya watsar da ita. A takaice dai, da ba don su Dangote sun sa baki ba, da tuni Sarkin Sunusi ya zama tsohon Sarki tun akaron farko da aka so tsigeshi.
Gangarar da nake so na rufe da ita shine, ya kamata a yi zama da duba na nutsuwa akan matsayi da darajar Masarauta a Arewa musamman ta Kano. Dole ne a futo a tura kudurori masu karfi da za a cire ikon kowanne gwamna akan makomar mulkin duk wani sarki da ke jiharsa. Ya kamata zabin sarki ya zama tsarin da al’umma suke da iko mai karfi akan sa, hakanan tsigeshi.
Wannan abu da Ganduje yayi duk da an bijirewa hukuncin kotu akan kar a yi nadin, hakanan a yanzu wasu manyan hakimai hudu a fadar Kano sun kuma makashi a kotu don warware tsarin da yayi, ba karamin nakasu bane da kuma ci baya ga kare daraja da hadin kan al’umma.
Wannan abu da aka yi, zai kawo rashin jituwa, kashe kudi, raba kan al’umma, kara cusa siyasa a cikin sarauta da sauran matsaloli da suka hada da rusa tarihi da makomar al’umma.
A karshe ina so mutane su gane cewar duk wannan hali da ake ciki na lalacewar abubuwa a Arewa da wasu yankuna, don rashin bawa sarakuna wata dama da za su taka ce wajen gudanawar rayuwar al’umma. Duk da cewar LG reforms da Murtala yayi a 1979 ya rage musu iko, amma duk da haka akwai yanayi da dama da tilas a dawo musu da damarsu. Yanzu ba wani abu da gwamnati za ta yi, ba tare da ta nemi hadin kai sarakuna ba. Idan kuwa har hakane ai ya kamata ace suna da matsayi da kariya mai karfi gami da rawar da za su taka karkashin doka don ganin an samu al’umma mai inganci da kuma hadin kai da za su yi kishin kansu da al’adunsu gami da asalinsu!
Discussion about this post