Dalibin nan dan shekara 15, mai suna Ekele Franklin, wanda ya samu sakamako mafi daraja a jarabawar JAMB, zai samu shiga jami’a a cikin 2019.
Franklin wanda dan asalin Jihar Imo ne, ya samu maki 347, kuma ya nemi shiga Jami’ar Lagos.
Sai dai kuma murna ta koma ciki, shi da iyayen sa, yayin da Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, Farfesa Ishaq Oloyede ya ce ba zai samu shiga a 2019, saboda bai kai shekaru 16 kamar yadda ka’idar shiga jami’a ta gindaya ba.
Yanzu wata jami’a mai zaman kanta, Gregory University da ke Uturu, Jihar Abia, ta amince ta dauke shi da gaggawa.
Shugaban Jami’ar, Gregory Ibe ne ya umarci a dauke shi nan take. Sannan kuma ya ce ba zai rika biyan kudin makaranta ba.
Maimakon haka, za a ma rika biyan sa kudaden tallafin yin karatu. Haka jami’in yada labarai na jami’ar, Ogbonnaya Ogwo ya shaida wa PREMIMUM TIMES.
Har ila yau, Jami’ar Gregory ta kuma ce za ta dauki wanda ya zo na biyu a kasar nan wajen yawan maki a jarabawar JAMB, wato dan Jihar Abia, mai suna Emmanuel Chidebube, mai shekaru 16.
Chidebube, ya samu maki 346 ne, wato da maki daya tal Franklin ya tsere masa.
Daga nan sai shugaban jami’ar ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta cire ka’idar daukar dalibi jami’a ba, wadda ta nuna ba za a iya daukar mai shekaru 15.
Ya ce yin haka na dankwafar da kananan yara masu kaifin basira matuka, kuma ba hanyar ci gaban al’umma ba ce.