Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya maka jaridar THE PUNCH kotu, tare da neman diyyar bata masa suna da zubar masa da mutunci da jaridar ta yi.
Obasanjo ya na neman diyyar ce a kan THE PUNCH da kuma wani fitaccen marubucin ta mai rubutu mako-mako, wato Sola Olumhense.
Ya na neman a biya shi zunzurutun kudi har naira bilyan daya, saboda nauyi da munin cin mutuncin da ya ce an yi masa.
Ya kai karar ce a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, dangane da rubutun da Sola Olumhense ya yi a kan sa, a ranar 17 Ga Janairu, 2019.
Rubutun mai take a Hausance, “Wannan ce iyakar gudummawar da Obasanjo zai iya bayarwa”, shi Obasanjon ya ce duk abin da aka rubuta a kan sa ba gaskiya ba ce.
Obasanjo ya ce: ” Jaridar PUNCH ta buga karairayin da Sola Olumhensen ya rubuta a kai na, wadanda babu gaskiya a ciki, bata min suna ne, babu hujjoji, cin mutunci ne, zubar min da girma ne, munanan kalamai ne, gilla ce, kuma sun ja jama’a na gudu na tare da tozarta ni.
“A cikin rubutun, Olumhense ya nuna cewa Obasanjo na nuna wa duniya cewa shi mutumin kirki ne, amma ba haka ya ke ba.”
Tsakure daga kadan daga rubutun da Olumhense ya yi, ya nuna cewa Obasanjo ya nuna wa duniya kafa Hukumar EFCC da ICPC don hana cin hanci da rashawa, amma ba da wannan manufar ya kafa ta ba.
Ya ce Obasanjo ya kafa EFCC da ICPC don su zame masa karnukan farautar wadanda ba su shan inuwa daya da shi.
“Sai abin da ya ke so suke yi masa, ba abin da ya dace ya rika yi da hukumomin ba a lokacin da ya ke mulki.”
Olumhense ya ce Obasanjo ya kirkiro batun farautar kudaden da aka ce marigayi Janar Sani Abacha ya wawura ne, don kawai ya yi masa bi-ta-da-kullin daure shi da Abacha ya yi.