Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, kuma Sarkin Anka, Mai Martaba Attahiru Ahmad, ya bada shawarar cewa a toshe dukkan layukan wayoyin da ke Jihar Zamfara idan ana so a dauko hanyar magance garkuwa da mutane a Jihar.
Sarki Attahiru ya ce saboda ta wannan hanya ce kawai masu garkuwa ke iya tuntubar iyalan wanda suka kama, har su kira su bukaci a biya su diyya.
Idan har za a toshe layukan waya tsawon watanni shida ko watanni uku a Jihar Zamfara, to za a samu babbar nasara. Saboda idan an yi haka, su kan su masu kira ‘yan bindiga su na ba su labarin halin da jami’an tsaro su ke ciki, ba za su iya ba kenan.”
Ya ce idan aka toshe layukan waya, kuma sai jami’an tsaro su datse hanyoyin da maharan ke boyewa, duk wanda aka ya fito ko zai shiga, sai a damke shi.
Ya ce garkuwa da mutane ta zama harkar neman kudi a Jihar Zamafara. Abin ya kai lalacewar da har za a rika yin garkuwa da mutane ana neman diyyar abinci ko katin waya (recharge cards) kafin a saki mutum.
Da ya ke jawabi a lokacin da Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurrahman Dambazzau ya kai ziyara a fadar sa, sarkin ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da a kafa Gagarimin Kqamitin Bincike, wanda zai gano dukkan masu hannu a wannan fitina a Jihar Zamfara, a hukunta su.
“Mu dai ba za mu taba yafe wa duk wani da ke da hannu wajen haddasa wannan fitina da ke haifar da kashe mutane da kona musu gidaje da raba dubban mutane daga gidajen su ba.
” Sun karkashe mutane, sun raba su da gidajen su kuma an hana dubbai gudanar da harkokin neman abincin su.”
Sarkin na Anka ya yaba da wasu matakai da aka dauka ba dakile hanyoyin da mahara ke samun abinci da fetur din da su ke zuba wa baburan su mai. Ya ce hakan ya kashe musu kaifin azamar yawan kai hare-hare barkatai.