TIRKASHI: Yadda masu garkuwa suka sace sirikin Buhari, Magajin garin Daura a Daura

0

Abu kamar almara, sai gashi mahara sun far wa garin Daura wato mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari sannan suka yi garkuwa da magajin garin Daura kuma sirikin sa, Musa Umar.

Kamar yadda aka ruwaito yadda abin ya faru, shi dai Umar ya dawo masallaci daga sallar magariba ne, daga nan sai ya zauna tare da jama’a suna tattaunawa a kofar gidan sa, kwatsam sai mahara suka afko cikin mota kirar Fijo 406.

Maharan sun rika harbi sama don tsorata mutane inda daga nan sai suka yi garkuwa da Magajin Garin Daura Umaru.

Shugaban Karamar hukumar Daura da dubban mutane sun hallara gidan sa domin yi wa iyalan sa jaje da Allah Kyauta.

Ayyukan masu garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a yankin musamman Arewacin Najeriya.

Jihohin Zamfara, Kaduna da Katsina ne suka yi kaurin suna da fama da ayyukan mahara da masu garkuwa da mutane.

Share.

game da Author