TAMBAYOYI 10: Shekaru hudu bayan hawa mulki, Buhari bai gamsu cewa rayuwar talaka ta samu canji ba

0

Ranar Litinin a wurin taron shan-ruwa a Fadar Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadin sa dangane da tsananin kuncin fatara da talaucin da ya ce ya gani da idanun sa talakawa na fama da ita.

Ya kuma nuna takaici ganin yadda kananan yara almajirai ke yawo cikin yagaggun tsummokara, rike da kwanukan roba, su na neman abincin da za su ci.

Buhari ya kara nuna takaicin abin da ya kira gazawar su manya da kuma rikakkun masu ilmi wajen kasa magance wannan babbar matsala.

Sai dai kuma masu karatu da dama su aiko da tambayoyi a dalilin wannan kalamai da Buhari yayi inda muka hada su don watso muku.

TAMBAYOYI GOMA

1 – Shin ba Buhari ne ya shafe shekaru 12 ya na takarar neman shugabancin kasa domin ya gyara wadancan matsalolin da ya lissafa ba?

2 – Shin Buhari bai yi kukan rashin samun damar hawa mulki ya gyara wadannan matasloli ba a 2011 bayan ya fadi zabe?

3 – Shin ba talakawa iyayen wadannan kananan yaran ne masu fama da kuncin talauci su ka rika jajircewa a duk lokacin zabe su ke zaben sa ba?

4 – Ko kuwa ba talakawan ne ’yan-a-mutun-Buhariyya ba, har sai da ta kai su na taimaka masa da kudin kamfen ba?

5 – Shin da Buhari ya samu nasara a 2015, wasu talakawa ba su kashe kan su a wajen murna ba?

6 – Da Buhari ya hau mulki, ya iske Gwamnatin Goodluck Jonathan ta dauko hanyar magance barace-barace a Arewa. Har ta fara gina makarantun almajirai na zamani. Me gwamnatin Buhari ta yi? Raya makarantun ta yi ko kuwa barin su aka yi suka mutu?

7 – Tausayin talakawa ne kara wa fetur kudi daga naira 87 zuwa naira 145, ko kuwa tausayin talakawa ne karin kudin tafiya Hajji daga naira 850,000 zuwa milyan daya da rabi?

8 – Shin ‘Trader Moni’ da ake yi, ya na kaiwa har cikin karkara, ko kuwa cikin birane kadai aka rika gudanar da shi, na cikin birni na amfana?

9 – Ta ya gwamnatin Buhari ta yi sakaci aka sace shanun Fulani a Arewacin Najeriya da Arewa ta Tsakiya, har Fulani suka fantsama fashi da garkuwa da mutane?

10 – A wurin taron shan-ruwan Buhari ya nuna cewa yawancin ayyukan raya al’umma duk Mataimakin sa Yemi Osinbajo ne ya rika kirkiro su. Shin dama bai hau mulki da kwakkwaran tsarin inganta rayuwar talakawan ba ne?

Tambayar Karshe: Ya aka yi shekaru hudu bayan hawan mulki, shi kan sa Buhari bai gamsu cewa rayuwar talakawa ta samu canji ba?

Share.

game da Author