TAMBAYA:Shin yin ‘Auren hannu’ da kallon fina-finai na rawa da tsiraici na karya azumi da yin kaffara? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA:Shin yin ‘Auren hannu’ da kallon fina-finai na rawa da tsiraici na karya azumi da yin kaffara?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Masturbation ‘Auren Hannu’: shi ne Wasa da Al’aura, wanda a larabce aka sansa da “Istimna’i”. Wannan yana nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima’i ga mutum da kansa da tunanin saduwa.

Hukuncin wannan (Istimna’i) da kallon tsiraici a musulunci Haramun ne kuma abin kyama ne. Hakika Haramcinsu na tsananta a cikin wata mai
alfarma. Suna kekasar da zukata, kamar yadda suke rage Imanin bawa.

Wannan munanan dabi’u ta masturbation (Istimna’i) da kallon tsiraici sun karya azumi matukar anyi maniyyi. Amma idan mutum bai fitar da
maniyyi ba, to azuminsa nanan tare da cewa ya aikata mummunan laifin da Shari’ah ta Haramta.

Hukuncin mutumin da ya karya azuminsa da masturbation (Istimna’i) ko kallon tsiraici ko dukkanin wani abunda ya motsa sha’awa har akayi
maniyyi shi ne kamar haka:

1) Ya tuba zuwa ga Allah domin ya aikata harumun, kuma ya keta al-farman Ramadana.

2) Zai kame bakinsa duk da cewa azuminsa ya baci.

3) Zai rama azumin wannan rana (kadai) da ya bata.

4) Kuma zai gaggauta tuba da rama azumin.

5) Amma babu kaffara a kansa, domin ba jima’i ya yi ba.

Allah shi ne mafi sani. Allah ka tsaremana Imaninmu da mutuncinmu. Amin.

Share.

game da Author