Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, tayi kakkausar suka a kan Shirin Inganta Rayuwar Talakawa da aka fi sani da ‘Social Intervention Programmes (SIP).
Aisha ta yi suka kan cewa duk da an kashe wa shirin naira biliyan 500, har yau babu wata alamar da ke nuna cewa shirin yayi wani tasiri a rayuwar talakawan Arewa.
Ta ce shirin har yau bai kai ga talakawan da aka kirkiri shirin domin su ba, musamman a jihohin Kano da Adamawa.
Duk da cewa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya kirkiro shirin, kuma shi ke kula da shi, Aisha ta zargi Shugabar Shirin SIP, Maryam Uwais da kasa yin wani katabus, duk kuwa da bimbin kudaden da aka ce an kashe.
” Na tabbatar da cewa miji na ya yi niyyar nada wani shugabancin SIP ne daga Kano, saboda dimbin yawan al’ummar jihar da kuma tasirin da suka yi a wajen zaben sa.”
Haka Aisha ta bayyana a wajen wani taron da ta yi da mata a fadar shugaban kasa.
Ta ce ta ji labarin wai mata 30,000 za su karbi naira 10,000 kowanen su a jihar Adamawa, amma fa kalilan ne suka amfana duk kuwa da cewa shirin har ya kai shekara uku kenan.
Ta ci gaba da cewa da dadewa ba ta gamsu da yadda ake tafiyar da shirin na SIP ba, amma ba ta son yin magana ne, don kada a ce ta cika surutai barkatai.
Sai dai kuma ta ce yayin da ta yi wani bincike a Kano da Adamawa kadai, ta gano cewa ba a aiwatar da shirin ta yadda ya dace ba.
” Kwanan nan na ga wani dattijo a Kano, ya na saida wasu ‘yan kaya. Na tambaye shi nawa ne jarin sa? Ya ce min tsakanin naira 2,000 zuwa naira 4,000. Kada fa ku manta mun yi kamfen muka yi wa talakawa alkawarin cewa za a rika raba musu naira 5,000 duk wata.
” Don haka ni dai ban san inda SIP ya yi wani tasiri ba. mai yiwuwa ya yi tasiri a wasu jihohi. Amma dai a jiha ta, Karfamar Hukuma daya ce tal daga cikin 22 ta ci moriyar shirin.
“Ban tambayi abin da ya faru ba, kuma ba so na ke na sani ba. Amma dai kasancewa shirin bai yi tasiri a jihar Kano ba, babbar alama ce da ke nuna cewa tabbas akwai gagarimar matsala a tafiyar da shirin kenan.” Inji Aisha.
Aisha ta kuma soki ikirarin da gwamnati ta yi cewa an kashe naira bilyan 12 da kuma dala milyan 16 wajen sayen gidan sauro da kuma wasu kayayyaki.
Daga nan sai ta yi mamakin yadda za a ce an kashe dala milyan 16 cur wajen sayin gidan sauro aka raba wa jama’a.
MARTANIN MARYAM UWAIS
Maryam Uwais ta maida martani ga Aisha Buhari, inda ta nuna cewa Aisha din ba ta da masaniyar yadda ake gudanar da shirin da kuma aiwatar da shi har ma da yadda ake cin moriyar sa.
“Na yi amanna cewa idan da ta saurari bayanan da za a sanar da ita, da kuma a ce ta bi diggigin adadin wadanda suka amfana, ta za ta iya gano dukkan wadanda suka ci moriyar shirye-shiryen na SIP gaba daya.
Ta ce akalla kananan hukumomi 12 daga jihar Adamawa sun ci moriyar akalla shiri daga daga cikin hudu na Inganta Rayuwar Talakawa, wato SIP. Sannan kuma inji ta, wasu kananan hukumomin sun ci moriyar shirin duka hudu.
” Mu na da akalla mutane 290 da ke amfana a kowane wata a jihar Adamawa.
Mun dauki wadanda suka kammala digiri har 11,000 ana biyan su a jihar Adamawa, sannan kuma akwai wadanda ba su mallaki digiri ba har su 440.”
A bangaren ciyar da yara ‘yan makaranta kuwa, Maryam ta ce ya zuwa yanzu tun bayan farawa a cikin Oktoba, 2018, ana ciyar da makarantu gwamnati 1,054.
Ta ce shirin ya na fuskantar kalubale a kowace jiha, domin kasafin kudi ya nuna za a rika ware masa naira bilyan 500.
Amma kuma ba duka ake samu ba.
Discussion about this post