Sojoji sun kara zargin Kungiyoyin Agaji na goyon bayan Boko Haram

0

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta sake zargin cewa wasu Kungiyoyin Agaji da ban a Gwamnati ba da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas, su na yi wa kokarin kakkabe ta’addanci zagon kasa, ta hanyar goyon bayan Boko Haram.

Kakakin Yada Labarai na Sojoji, Sagir Musa ne ya sanar da haka a yau Alhamis, inda ya ce kamun da sojoji suka yi wa wani kwamandan Boko Haram mai suna Mohammed Madu a ranar Lahadin da ta gabata, ya tabbatar da haka.

Dama a cikin 2019 sai da sojoji suka yi irin wannan zargi a kan kungiyoyin agaji da ke aiki a yankin na Arewa maso Gabas, inda Boko Haram ke kai hare-haren ta’addanci.

Musa ya yi zargin cewa babban kwamandan Boko Haram da aka kama ranar Lahadi, dan bangaren mayakan Shekau ne.

Kakakin sojoji Sagir Musa ya tabbatar da cewa binciken farko da sojoji suka fara yi ya nuna cewa tabbas Boko Haram na bangaren Shekau na “samun agajin abinci da magunguna daga wasu kungiyoyin bada agaji da ke aikin agaji a yankin.”

Sagir ya ce wannan cin amanar kasa ne kuma barazana ce karara ga tsaron kasa.

Ya gargade su da su daina kuma rika aikin su kamar yadda dokar aiki a yankunan da ake fama da yaki ta gindaya.

Duk da dai bai bayyana kowace kungiya ba ce, Sagir ya kara da cewa daga yanzu jami’an tsaro ba za su sake sassauta wa wanda duk aka kama da wannan zagon kasa ba.

Idan ba a manta ba cikin Disamba 2018, sojoji sun dakatar da ayyukan hukumar UNICEF har sai yadda hali ya yi.

Amma daga baya gwamnatin tarayya ta gaggauta shiga tsakani, aka kashe maganar.

Share.

game da Author