Ranar Litinin mai zuwa ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin Shugabar Majalisar Dinkin Duniya (UN), Maria Espinosa.
Espinosa na kan hanyar zuwa domin kawo ziyarar yini daya a Abuja, Najeriya.
Kakakin Yada Labaran Espinosa, Monica Gravley ce ta fitar da wannan sanarwa a lokacin wani taron manema labarai a jiya Juma’a, a Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya, da ke New York.
Ziyarar da za ta kawo na daga cikin ziyarar kwanaki takwas da za ta karade kasashen tsakiyar Afrika ta Yamma, da ta fara a ranar Juma’a.
Sai dai kuma Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya tambayi dalilin zuwan ta Najeriya, amma bai samu cikakkiyar amsa ba.
Sai dai kawai kakakin ta yi alkawarin rika sanar da manema labarai dukkan abubuwan da aka tattauna a kai a kai.
Gravley ta ce dukkan ministocin Buhari za su taya shi tarbar Shugabar ta Majalisar Dinkin Duniya, wadda bayan saukar ta za gana da daliban Jami’ar Abuja.
Daga nan kuma za ta gana da jami’an Majalisar Dinkin Duniya masu aiki a Najeriya kuma za ta gana a kan wata tattaunawar musayar ra’ayi da za a yi a kan gudummawar mata.
Tattaunawar ta kunshi batun rawar da mata za su taka wajen haduwar karfi da karfen kasashen duniya domin cimma wata manufa.
Taron zai za hankali wajen kokarin muna muhimmancin a gudu tare a kuma tsira tare, ba wai kowace kasa ta kama tsagin gaban ta wajen tunkarar wani babban kalubale ba.
Sai dai kuma wannan gamayya na fuskantar babban kalubale, ganin yadda Amurka ke amfani da karfin sojan ta wajen daukar hukunci ita kadai, ba tare da jin sahwarar Majalisar Dinkin Duniya ba.
Dalili kenan ma wasu manyan kasashen irin su Chana da Indiya suke cewa idan haka ne, to mene ne amfanin Majalisar Dinkin Duniya kuma?