Babban Daraktan Jami’an Tsaro na SSS, Yusuf Bichi, ya danganta wasu daga cikin matsalolin tsaron da ake fuskanta a kasar nan, da yadda shugabannin siyasa su ka fi gaskata bokaye da matsibbata fiye da jami’an tsaro.
Ya ce ‘yan siyasa da dama sun mika rayuwar su kacokan ga bokaye da matsafa domin magance musu matsalar tsaro.
Bichi ya yi wannan jawabi ne a wurin Taron Sanin Makamar Aiki da aka Shirya wa Gwamnoni Zababbu da kuma wadanda za su sake zarcewa.
Ya ce har zolayar ‘yannsiyasa ya kan yi ya na ce musu kun fi amanna da bokaye.
“Su kawai da wani boka ko dan duba ya ce musu wani abu zai faru a kan mukamin da ka ke, to idan abin ya faru, shikenan sai mutum ya mika kai kawai.”
Ya yi korafin cewa akwai wawakeken gibin rashin samun bayanan sirri daga karkara saboda akwai gibi tsakanin shugabannin siyasa na kuma shugabannin gargajiya.
Discussion about this post