Shugaban masu dafa abinci na Gidan Gwamnatin Jihar Barno, ya rataye kan sa

0

Babban kukun kuma shugaban masu dafa abinci a Gidan Gwamnatin Jihar Barno, ya rataye kan sa a cikin fadar gwamnatin.

Ma’aikacin mai suna John Achagwa, ya rataye kan sa ne a wani reshen bishiyar da ke cikin gidan gwamnatin.

Har zuwa yanzu dai babu wanda ya san dalilin da ya sa Achagwa ya rataye kan sa.

Sai dai kuma abokan aikin sa sun bayyana cewa sun fahimci ya na cikin bacin rai tun daga safiya har zuwa rana.

Sun ce daga lokacin ne kuma ba su sake ganin sa ba, aka rasa inda ya yi.

Amma wani abokin aikin sa da ba ya so a bayyana sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya ga Achagwa cikin matukar damuwa tun safiya har lokacin da aka daina ganin sa.

“ Akwai ma lokacin da zo ya nuna min wata lamba a cikin wayar sa, ya ce ya na so na goge lambar daga cikin wayar sa. sai na ce masa ban san yadda ake goge lamba daga cikin kowace waya ba.

“ Mu na tare da shi har wajen karfe 1:30 na rana. Daga nan muka tafi sallah da Azahar. Da muka dawo muka neme shi muka rasa. Mun dauka ya dan kewaya wani wuri ne kawai, ko kuma ya fita waje. Sai daga baya wani ya kira mu ya ce ga wani mutum can ya rataye kan sa a bayan masaukin bakin Gidan Gwamnati.

Wadanda suka san Achagwa sun shaida cewa ya yi ritaya daga aikin cikin gidan gwamnatin tun shekaru uku da suka gabata, amma aka sake daukar sa dadin girkin da ya ke hadawa.

An kwanto gawar sa daga kan bishiya kimanin karfe 3:30 na yamma.

Mamacin ya yi aiki da dukkan gwamnonin farar hula a Gidan Gwamnatin Barno.

Share.

game da Author