Shin Alkalai, Lauyoyi Da ‘Yan sanda Suna Taimakawa Gurin Ci Baya Na Yaki Da Miyagun Ayyuka a Nijeriya? Daga Kais Daud Sallau

0

Nijeriya ta dade tana fama da yawaitar miyagun ayyuka wanda akasari matasa ne ke aikata wannan aikin, gwamnati na iya kokarin ta taga da daidai al’amura, amma abin da wuya. Wadannan miyagun ayyukan sun hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, sara suka, satan shanu, yan kungiyar asiri, cin hanci da rashawa, rikici kalilan ci ko na addini, ta’addanci da sauran su.

Ba shakka wadansu alkalai suna da rawar da suke takawa gurin kawo ci baya a gurin yaki da miyagun ayyuka a kasar nan. Dayawan lokaci zaka ga an kama mai laifi, an kai shi kotun sai kaga an dauki shekara masu yawa ba’a yanke shari’a ba. Wani lokaci shi mai laifin ya kan amince yayi laifin, amma sai kaga ana ta jan shari’a har wata rana kaga an sake shi.

Misali idan muka dubi shari’a da akeyi wa shareren mai yin garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadikeda (Evans) da tawagar dan-sanda Abba Kyari suka kama da yaran shi da suke garkuwa da mutane tare, yau kusan shekara biyu kenan ba abinda aka yi a shari’a su, ba’a yanke shari’ar su a kotur na farko ba, balle aje kotur daukaka kara zuwa kotur koli. Allah ya kiyaye ba abin mamaki ba ne wata rana kaji an ba da belin su.

Mu koma zuwa ga yaran da aka kama da zargin su suka kashe babban sojan nan General Alkali a jihar filato, suma wai an ba da belin su, kuma shikenan maganar ta mutum kenan. Wanda kuma ance duk wanda ake zargin shi da kisan kai (Criminal Case) ba’a ba da belin shi sai yana fama da rashin lafiya mai tsanani.

Jan lokacin mai tsawo a gurin shari’a da ba da beli ga mutanen da basu cancanci a ba da belin su ba da wadansu alkalai Nijeriya suke yi, yana daya daga cikin dalilin da yake kawo koma baya gurin yaki da miyagun ayyuka a Nijeriya.

Haka suma wadansu lauyoyi suna da nasu gudumawa da suke bayarwa gurin kawo cikas da yakin da miyagun ayyuka da ake yi a kasar nan, zaka ga lauya ya tabbatar da wannan mutum mai laifi ne, kuma shi mai laifin ya amince yayi laifi, amma sai kaga lauya yana ta kawo wadansu dalilai na banza domin bata lokacin gurin yanke shari’a. Wani lokacin ma ta hanun Lauyoyin ake hada baki da alkhairai domin ba da belin mutumin da ake zargi da kisan kai wanda lauyan da shi alkalin sunsa ya taka doka. Idan gwamnati ta dauki mataki akan alkalai da Lauyoyin da ake zargi da saba doka, sai ance ba’a ba sashin shari’a gashin kanta kamar yadda doka ya tana da ba. Toh tunda ba’a hukunta mai laifi yadda ya kamata, toh dole abu ya kara ci gaba. Allah ya kiyaye.

Haka suma yan’sanda wadansu lokutan idan suka maka masu laifi, ba za su kai su kotur ba, sai su karbi wani abin goro daga hanun masu laifin su sake su, su kuma sai su je su ci gaba da miyagun ayyuka da suka saba domin sunsan ko an kama su, kudi kawai za su biya a sake su. Toh wannan shima yana taimakawa gurin rashin nasara da yaki da miyagun ayyuka da ake yi.

Kuma wannan halai wanda su alkalai, lauyoyi da yan’sanda suna taimakawa gurin rashin goyon bayan da al’ummar gari suke kin ba hukuma, domin mutum yana tsoro sai ya bayar da bayanai akan masu aikata miyagun ayyuka, idan aka kama su, kwana biyu sai a sake su. Sai su zamawa mutanen da suka nuna su baraza na, wadansu lokutan su kashe su.

Saboda haka idan har ta tabbata mun amince mu yan Nijeriya ne, kuma muna kishin kasar mu, kuma muna son kasar mu ta ci gaba, sannan muna son kasar mu ta zauna lafiya, toh dole zamu yi aiki tsakanin mu da Allah, mu san cewa wannan miyagun ayyuka sun shafe mu, domin idan bai taba ka ba, ya taba dan-uwanka, ko dan garin ka, ko dan jihar ka, ko dan kasar ka, ko dan addinin ka ko kabilar ka.
Dole zamu cire sun zuciya, kabilanci, addinanci ko bangaranci mu ya ki wannan matsalar.

Muna rokon Allah ya kawo mana saukin miyagun ayyuka da muke fama da su. Su kuma masu aikata wannan ayyukan Allah ya shirye su, wadanda ba masu shiryuwa ba ne, Allah yayi mana maganin su. Mun da Allah bai sa muna cikin su ba, Allah ya kara kare mu. Allah ya ba mu zaman lafiya a kasar mu. Ya bamu damini mai albarka. Amen.

Share.

game da Author