SHARI’AR ZAMAFARA: Oshiomhole ya ce Kotun Koli ta damka mulki ga ‘bakin-haure’

0

Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshimhole, ya bayyana cewa Kotun Koli ta yi rashin adalci inda ta bai wa jam’iyyar PDP gaskiya a shari’ar zaben gwamnan Jihar Zamfara.

Oshiomhole ya yi wannan jawabi ne bayan kammala taron Shugabannin Kwamitin Gudanarwar APC, a hedikwatar jam’iyyar a Abuja.

Shugaban na APC ya ce damka nasarar a hannun PDP ya nuna tamkar an mika mulkin jihar Zamfara a hannun abin da ya kira ‘bakin-haure’.

Daga nan sai ya ce kamata ya yi kotu ta ce a sake zabe, ba wai ta damka wa PDP mulki a bagas ba.

Sai dai kuma ya ce amma tunda babu yadda za a yi a daukaka karar hukuncin da Kotun Koli ta yanke, to ya bar wa Allah kawai.

Oshiomhole ya ce ba a yi wa daukacin al’ummar jihar Zamfara adalci ba, domin tun daga gwamna da sanatoci da mambobin tarayya da na majalisar dokokin jihohi, duk Kotun Koli ta dora musu wadanda ba su suka zaba ba.

“Babu adalci a inda kotu ta dora wa al’ummar jiha wasu ‘bakin-hauren’ da ba su aka zaba ba. Amma babu yadda za mu yi, tunda Kotun Koli ta rigaya ta yanke, babu yadda muka iya, sai dai mu bar wa Allah kawai.”

Sai dai kuma bai bayar da amsa ba, a lokacin da aka tambaye shi ko APC za ta hukunta ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka kai ta kara kotu.

Share.

game da Author