Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, wato JAMB, ta bayyana cewa akwai yiwuwar ta soke kusan rabin sakamakon jarabawar wadanda suka zauna a cikin watan Afrilun nan na 2019.
Wani babban jami’in hukumar ne wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES wannan bayani na soke sakamakon kusan rabin wadanda suka zauna jarabawar shiga Jami’a ta 2019.
An rubuta wannan jarabawa a fadin kasar nan tsakanin ranakun 11 zuwa 18 Ga Afrilu.
Majiyar PREMIUM TIMES ta ce yayin da aka samu fantsama da yawaitar satar jarabawa a dukkan fadin kasar nan, amma dai na wani bangaren ya fi na wani muni.
Ya ce irin yadda aka rika “nuna rashin tsoron hukuma aka rika satar jarabawa kiri-kiri a fili, zai rikita wa mutum kwakwalwa, musamman idan ya ji cewa har da iyayen yara ne ake hada baki, da kuma masu cibiyoyin da dalibai ke rubuta jarabawa.”
Sai ya kara haske da cewa wannan ne dalilin da ya sa aka samu jinkiri sosai na fitowar jarabawar.
Ya kuma ce ’yan Najeriya za su cika da mamaki idan aka ce za su samu damar kallon abin da kyamara ta rika ikodin ana yi, a lokacin da ake rubuta jarabawar.
Ya ce JAMB ta makala kyamarori a dukkan cibiyoyin rubuta JAMB 700 da ke fadin kasar nan.
Daga nan sai ya kara da cewa akalla za a soke kashi 50 bisa 100 na dukkan jarabawar da aka rubuta a wasu jihohin.
Kakakin Hukumar JAMB, Fabian Benjamin, ya tabbatar da gagarimar satar jarabawar da aka yi, amma ya ce hukumar JAMB ba za ta ware wani yankin kasar nan shi kadai ba.
Discussion about this post