Sanatoci na binciken nada sabon Shugaban NYSC ‘ba tare da bin ka’ida ba’

0

An umarci Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Matasa da Wasanni, da ya gaggauta binciko yadda aka nada sabon Daraktan NYSC.

An yi zargin cewa an nada Shuaibu Ibrahim ba bisa ka’ida ba.

Sanatan Shiyyar Kogi na PDP, Dino Melaye ne ya tashi ya karanto koken sa domin a cewar sa, akwai inda aka kauce hanya, wajen nada sabon Darakta Janar na NYSC.

Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Sagir Musa ne ya bayyana sanarwar maye gurbin Sulaiman Kazaure da Shuaibu Ibrahim.
Ya yi sanarwar ce a ranar 26 Ga Afrilu.

Dino Melaye ya bayyana cewa: “Akwai waskiya wajen yin wannan nadi, kuma duk Hafsan Hafsoshin Najeriya ya yi wannan waskiyar, wajen nada sabon Darakta Janar na NYSC.

“Sashen Doka na 5 ta NYSC ta ce Shugaban Kasa ne kadai ke da ikon nada Shugaban NYSC. Amma kawai Hafsan Hafsoshi ya bushi iska ya nada sabon Darakta Janar, kuma ya bushi iska ya cire wanda ke a kai.”

Dino ya ce dukkan Shugabannin NYSC da aka taba yi a baya, kowane shugaban kasa ne ke nada shi. Don haka Najeriya ba kasar da kowa ya hau mulki zai yi abin da ya ga dama ba ce.

“NYSC ba wani bangare ba ne na sojojin Najeriya. NYSC na cikin dokokin da Majalisar Tarayya ta shimfida.”

Nan take aka amince da korafin da Dino Melaye yayi, kuma aka nada kwamiti domin gudanar da bincike a cikin mako guda.

Share.

game da Author