Masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da mutane 16 a kauyen Zurmi jihar Zamfara sun bukaci a biya su Naira miliyan goma sha biyar kudin fansa kafi su saki mutanen dake tsare a wajen su.
Daya daga cikin ‘yan uwan mutanen da aka yi garkuwa da su ya bayyana haka ga wakilin PREMIUM TIMES ranar Laraba.
A hiran da suka yi da maharan ta wayar tarho shugaban kungiyar ya bayyana cewa Naira miliyan 3.5 din da aka biya a matsayin kudin fansa da farko ya zama lada inda ya yanzu haka suna bukata a sake biya su Naira miliyan biyar kafin su saki mutane 16 da suka kama.
A ranar 29 ga watan Janairu ne kungiyar masu garkuwa da mutane suka sace mutane 16 daga wannan kauye.
‘Yan uwa da abokan arziki sun yi karokaro suka hada Naira miliyan 3.5 wanda suka biya domin a sako ‘yan uwan su amma haka ya gagara.
A dalilin haka mazauna kauyen ke kira ga gwamnati da ta kawo musu agaji ganin cewa sun siyar da duk kadarorinsu ne wajen hada Naira miliya 3.5 din da suka aika wa maharan.
” A yanzu haka ba mu da sauran kadaran da za mu siyar muhada kudin da maharan ke bukata.
Mutanen da masu garkuwan suka kama sun hada da Sa’adatu Usman, Rafi’a Falalu, Abdulsamiu Ashafa, Abdullahi Marafa, Rufa’i Danwaya, Hadiza Auwalu, Safiya Sharif, Amina Sabiu, Lami Sidi, Marwa Sidi, Fatima Sidi, Hadiza Sidi, Bilyaminu Sarkin-Noma da matarsa Maryam Aliyu sannan da dansu mai shekara biyu.