1. Matsalar rashi da tsadar audugar mata ya sa mata ba su iya zuwa makaranta idan al’adar su ta
Binciken ya nuna cewa akalla mace daya cikin mata 10 bata iya zuwa makaranta na tsawon kwanaki hudu zuwa biyar duk wata. Wanna ba ga ‘yan mata ya tsaya ba har da matan aure.
Bincike ya nuna cewa mata biliyan 1.2 a duniya na fama da wannan matsalar dake da nasaba da tsananin talauci.
2. Ana bukatan gina dakunan bahaya Miliyan 2 Najeriya duk shekara
Bisa ga sakamakon binciken da asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta fitar ya nuna cewa mutane miliyan 47 na bahaya a waje a Najeriya.
Domin samun nasara a manufar tsaftace muhalli nan da shekara 2019 zuwa 2025 UNICEF ta ce Najeriya za ta bukaci karin ban dakuna miliyan biyu duk shekara na tsawon shekaru bakwai.
3. Dalilan da yasa manyan asibitocin kasar nan ba su aiki yadda ya kamata
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa manyan asibitoci da suka hada da asibitocin koyarwa na jami’o’I za su fara aiki yadda ya kamata a kasar nan idan gwamnati ta inganta asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko
4. Kungiya ta yi Kira ga mutanen da su kula da lafiyar idon su
Kungiyar ‘Nigerian Optometric Association’ (NOA) ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan samar da kiwon lafiyar ido mai nagarta ga mutanen kasa.
Shugaban kungiyar Ozy Okonokhua ne ya yi wannan kira ganin cewa ba kowa bane ke iya samun wannan kulan a asibitocin kasar nan.
Okonokhua yace abin takaici ne yadda mutane musamman mazauna karkara ke makancewa saboda rashin samun ingantaccen kulawa.
5. Rashin isassun magunguna da kula na yi wa yaki da cutar kafar angulu a Najeriya
Malaman asibitin sun bayyana cewa rashin samun maganin cutar kai tsaye da asibitocin yin gwajin cutar na daga cikin matsalolin da suka hana kasar nan kubuta daga kangin da take fama dashi game da yaduwar cutar.
Jami’in cibiyar hana yaduwar tarin fuka da kanjamau dake Amurka Odume Betrand yace babban abin takaici shi ne yadda mutane ke yawan dogaro da allurar rigakafin BCG da aka yi wa yara kanana a matsayin maganin kawar da cutar.
6. Ranar cutar koda: Muna kira ga gwamnati kan a rage farashin kula da masu cutar
Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta rage farashin samun kula da mutanen dake fama da cutar koda keyi cewa tsadar kudin magani yayi yawa.
Ma’aikatan kiwon lafiya sun yi wannan kira ne a ranar cutar Koda ta duniya ta hanyar wayar da wa mutane kai game da cutar da hanyoyin da za su bi don samun kariya daga kamuwa da cutar ganin cewa cutar na daya daga cikin cututtukan dake kisan mutane a duniya.
7. Najeriya na fama da karancin likitoci
Sakamakon binciken sanin yawan likitocin da Najeriya ke da su da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbata cewa fannin kiwon lafiyar kasar nan na fama da karancin likitoci.
Wakiliyar PREMIUM TIMES da ta gudanar da wannan buncike bisa rahoton hukumar yi wa kwararrun likitoci rajista na kasa (MDCN) ta gano cewa yawan likitocin da suka yi rajista da ita a yanzu haka sun kai 42,845.
Rahoton ya nuna cewa a duk shekara likita daya a Najeriya na kula da marasa lafiya 4,850 wanda hakan ya saba wa dokar aiyukkan likitoci da kungiyar kiwon lafiya ta duniya.
8. Muna rokon gwamnati da guiwowin mu a kasa ta rage kudin audugan mata
Wasu matasa maza da mata tare da hadin guiwar bayan wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi kira ga gwamnati kan ta rage farashin audugan da mata kan yi amfani da su a lokacin da suke jini na wata-wata ganin cewa audugan yanzu yayi tsadan da yakan gagari mata siya domin amfani da shi.
9. Masu fama da cutar Kanjamau na biyan Naira 2000 kudin maganin
Hadaddiyar kungiyar masu dauke da cutar kanjamau (NEPWHAN) ta koka kan yadda mamobinta masu dauke da wannan cuta ke biyan Naira 2000 duk wata domin samun maganin cutar a kasar nan.
Jami’in kungiyar reshen jihar Legas Peter Obialor yace a dalilin haka da dama daga cikin wadanda ke fama da cutar dake basu iya samun magani.
Sannan wani abin takaici shine hatta yin gwaji sai mambobin su sun biya da haka bai kamata ba.
10. Kashi 13 bisa 100 na matan da aka yi wa kaciya a Najeriya likitoci ke yi
Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun koka kan yadda yi wa mata kaciya ya zama ruwan dare duk da kokarin kawar da shi da ake yi a Najeriya.
Jami’in hukumar kidaya na majalisar dinkin duniya (UNFPA) Eugene Kongnyuy yace wani abin takacin shine yadda likitoci suka kwace wannan mummunar sana’ar daga hannun likitocin gargajiyya.
Ya ce bincike ya nuna cewa likitoci sun yi wa mata kashi 13 bisa 100 daga cikin adadin yawan matan da aka yi wa kaciya a kasar nan.
11. Yara sama da 900,000 na fama da matsanancin yunwa a Arewacin Najeriya
Asusun bada tallafi ga kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta koka kan yadda ake samun yawan yara da ke fama da matsanancin yunwa a yankin Arewa Maso Gabashin Kasar nan.
Jami’ar asusun Bamidele Omotola ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa sama da yara 900,000 na nan a jihohin dake arewa maso gabacin kasar nan kuma suna fama da matsinacin yunwa.