Rundunar Yan Sandan Jihar Filato ta tabbatar da kashe mutum uku da shanu 19, a wani sabon rikici da ya barke cikin Karamar Hukumar Bassa.
Kakakin Yn Sanda Tyopev Terna, ya ce an yi kashe-kashen ne a kauyukan Billi da Ariri.
Ya ce an kashe shanu 319 kwana daya bayan an kashe mutane uku tare da ji wa wani rauni a Miyango da Rotsu, wadanda kauyuka ne duk a cikin Karamar Hukumar Bassa.
Cikin sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES, Terna ya kara da cewa wasu makiyaya biyu kuma sun bace, har yau ba a san inda su ke ba.
Ya ce sun samu rahoton kai harin da aka kashe mutane uku a ranar 29 Ga Afrilu, sai kuma ranar 39 Ga Afrilu suka sake samun rahoton kashe shanu 319 tare da sace 11.
Fulani biyun da suka bace, matasa ne, Mubarak Yakubu da kuma Shehu Saidu.
Daga nan ya ci gaba da cewa ’yan sanda sun shiga neman wadanda suka bace din domin ceto to. Kuma ana kokarin kamo wadanda duk ke da hannu a kashe-kashen.
Sannan kuma an tara shugabannin kauyukan an ja kunnen su daga kauce wa tashe-tashen hankula.
Shugaban Miyetti Allah na Kasa Nura Abdullahi, ya zargi kabilar Irigwe da kashe-kashe da kashe shanun Fulani a Kuru kusa da Barkin Ladi da kuma Kwal cikin Karamar Hukumar Bassa.
Shi ma ya tabbatar da cewa Fulani sun rasa shanu sama da 300 da aka kashe baya kuma ga wadanda aka sace.
Sai dai kuma shugabannin MACBAN din ciki har da Alhaji Usman, sun roki Fulani kada su dauki fansa, su hakura tunda hukuma ta shiga tsakani.
Amma kuma wani shugaaban kabilar Irigwe mai suna David Kinge, yace ba gaskiya ba ne, ba a kashe shanun kowa ba.
Discussion about this post