RASHIN TSARO: Daura ta janye yin hawa da shagulgulan Sallah Karama

0

Masarautar Daura ta bada sanarwar janye yin hawa da shagulgulan Sallah Karama, wanda za a fara cikin mako mai zuwa.

Danejin Daura, Abdulmumin Salisu ne fitar da wannan sanarwa a madadin masarautar Daura a yau Litinin.

Garin Daura, wanda nan ne cibiyar Masarautar Daura, can ne mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda aka sace Magajin Garin Daura, ranar 1 Ga Mayu, aka gudu da shi, kuma har yau babu labari.

Magajin Garin Daura Umar Musa kani ne uba daya da Sarkin Daura na yanzu, kuma shi ne basarake na biyu mafi girma a masarautar Daura.

Baya ga cewa ya na auren ‘yar yayar Shugaba Buhari, har ila yau Magajin Garin na Daura siriki ne ga Babban Dogarin Buhari.

Danejin Daura Salihu ya bayyana cewa an janye hawan sallah saboda tabarbarewar tsaro a wasu yankunan jihar Katsina.

Ya ce bayan sallar Idi, za a yi addu’o’i domin neman samun zaman lafiya a jihar Katsina da ma kasa baki daya.

Daga karshe ya umarci dukkan Hakiman Yankin 16 da Dagatai 245 su gudanar da addu’o’in zaman lafiya a fadin kasar nan.

Share.

game da Author