RASHIN TSARO: Buhari na ganawa da Gwamnonin Arewa

0

A yau Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Gwamnonin Arewacin kasar nan su kadai, domin tattauna matsalar tsaro.

Da ya ke wa manema labarai jawabi bayan fitowar su daga taron, Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari, ya ce gwamnonin sun je Fadar Shugaban Kasa ne dominn su roki ya sa baki danganec da matsalar tsaro da ta dabaibaye Arewa.

Ya ce sun tattauna matsalar Boko Haram a Arewa maso Gabas da kuma garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Ya kara da cewa gwamnonin sun nuna wa Buhari damuwar sa da kuma irin yadda ba a ganin wani hobbasa na shawo kan rikice-rikicen.

Ya ce nun nuna wa Buhari akwai matukar bukatar daukar matakan gaggawa domin magance wannan fitina tun kafin ta kai ga yin muni kamar Boko Haram.

Masari ya kara shaida cewa gwamnonin sun kuma kawo shawarar yadda za a kawo karshen matsalar.

Dangane da abin da Buhari ya ce zai yi domin gaggauta shawo kan matsalar, Masari ya ce ba abu ne da za a bayyana a fili ba.

Idan ba a manta ba, har sirikar Gwamna Masari sai da masu garkuwa suka taba sacewa a ranar 9 Maris. Ta shafi sama da mako daya ba a ceto ta ba, har sai bayan da aka biya diyyar naira milyan 30.

Share.

game da Author