Domin hana yaduwar cututtuka da kare kiwon lafiyar ma’aikatan kiwon lafiya a lokacin da suke gudanar da aiyukkan hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta tsara wani shiri da ta yi wa suna ‘Turn Nigeria Orange’ da zai sa a rika horas da ma’aikatan asibiti game da muhimmancin wanke hannaye a kowani lokaci.
Shirin ya kunshi samar da ruwa da sabulu a asibitocin kasar nan sannan da horas da ma’aikatan kiwon lafiya da su runguma dabi’ar yawan wanke hannaye a kowani lokaci don tsaftace kan su.
Shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattawa Lanre Tejuoso ya kaddamar da shirin a babbar asibitin koyarwa na jami’ar Abuja a taron ranar wanke hannu da ake a duk ranar 5 ga watan Mayu na kowace shekara.
Tejuoso ya ce babu dadi ganin yadda ma’aiakatan asibiti ke fadawa halin ha’ula’i a dalilin kamuwa da cutuka a wajen yin aikin su
Ya ce a dalilin haka NCDC ta shigo da wannan shiri domin ‘rigakafi ta ya magani’.
Bisa binciken da NCDC ta gudanar an gano cewa kashi 15 bisa 100 na maza da kashi 5 bisa 100 na mata a Najeriya basa wanke hannayen su bayan sun yi amfani da makewaya.
”Rashin wanke hannu da ruwa da sabulu ba da ruwa ba kawai na sa a kamu da cututtuka kamar su amai da gudawa, mura, da sauran su.”
Bayan haka shugaban NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce NCDC yace idan ba a manta ba tsakanin shekarar 2018 da 2019 adadin yawan a’aikatan kiwon lafiya da kasar nan ta rasa sun kai 40 a lokacin da zazzabin lasa ya bullo.
Ya ce haka na da nasaba ne da rashin wanke hannaye da wasu ma’aikatan kiwon lafiya ba su yi.
A dalilin haka NCDC ke kokarin ganin ta dakile yaduwar cututtuka ta hanyar wayar da kan ma’aikata game da mahimmancin wanke hannaye musamman da ruwa da sabulu a kowani lokaci musamman idan aka fito daga bayan-gida.