An fara rantsuwar Shugaba Muhammadu Buhari da karfe 10:30 na safiyar ranar 29 Ga Mayu, ranar da daukacin dukkan ’yan Najeriya ke jira su ji sabbin alkawurra da kuma kudirorin da Buhari zai bayyana cewa su ne zai yi wa jama’a albishir da su.
Sai dai kuma abin mamaki, bayan da Cif Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya kammala rantsar da shi da Mataimakin sa Yemi Osinbajo, Buhari bai yi wani jawabi ba, sai kawai ya haye budaddiyar mota, aka rika zagayawa da shi, kamar yadda aka saba yi a al’adance.
Yayin da aka rantsar da Buhari a karo na farko, ya yi jawabi masu ratsa jiki, inda ya nuna cewa: “Ni na kowa ne, kuma babu wanda zai ce shi ne ke da ni.”
Sannan kuma ya bayyana muhimman kudirorin sa uku da ya ce su ne zai fi maida hankali a kan su; wadannan kuwa sun hada da yaki da cin hanci da rashawa, inganta tsaro da kuma farfado da tattalin arziki.
Yayin da ya cika shekaru hudu cur a kan mulki, kuma ya sake yin nasara, ‘yan Najeriya na da hakki su ji daga gare shi shin ko ya yi nasarar cimma kudirorin nan uku da ya sha alwashi a ranar da rantsar da shi a cikin 2015? Wane ci gaba aka samu? A wannan sabon zango kuma na biyu da aka shiga daga jiya 29 Ga Mayu, wadanne kudirori Buhari ke dauke da su.
Duk ba a ji wadannan ba, kuma babu wanda ya yi wa jama’a bayanin dalilin da ya sa Buhari bai yi jawabi ba.
Wannan ne karon farko a tarihin kasar nan, wasu ma sun ce tarihin kafuwar dimokradiyya a duniya, a ce an rantsar da shugaban kasa, amma bai yi wa al’ummar kasar jawabin abin da ya ke dauke da shi na shekarun wa’adin da zai tunkara ba.
Bai yiwuwa a ce mantuwa ce. kuma ba zai yiwu a ce ba a shirya ba. Sannan kuma ganganci ne ko wauta a ce wani jami’in sa ne ya mato kwafen takardar da Shugaban Kasa zai karanta bayan rantsar da shi.
To idan har tun farko dama Buhari bai je filin rantsarwa da niyyar karanta jawabi ba, mene ne dalili?
Sannan kuma me ya sa ba a bada hakuri a lokacin ba, kuma ba a yi sanarwa ba daga bisani?
Kada fa a fara jefa kafa cikin ‘Next Level’ a halin magagin barci.
Shugaban Kasa ya fahimci cewa a matsayin sa na direban fasinjoji kusan milyan 200, wannan ne lodin sa na karshe.
Da ya isa cikin tashar sauke fasinja a 2023, to za a karbe masa lasisin tuki, kuma za a karbe motar daga hannun sa, a damka wa wani sabon direba.
Ya wajaba Buhari ya rika tuki da kula, a cikin natsuwa, ba kamar lodin farko da ya yi na fasinjan 2015, inda ya rika tuki ya na waiwaye har ya na ruftawa cikin ramu da shiga gargada ba.