RANAR MA’AIKATA: Gwamnatin Kano ta soke fifiko tsakanin mai Digiri da mai HND

0

Gwamnatin Jihar Kano ta soke fifikon da aka dade ana sa-tok-sa-katsi tsakanin mai digiri da kuma mai shaidar Babbar Difiloma, wato HND.

Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ne ya bayyana haka a wajen da ya yi jawabi a taron Ranar Ma’aikata, jiya Laraba a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Ganduje ya ce gwamnatin sa ta dauki wannan mataki ne domin karfafa guiwar ma’aikatan jihar su tashi yin aiki tukuru.

Daga nan ya ce gwamnatin Kano na aiki a ko da yaushe domin ganin ta kara faranta wa ma’aikatan jihar rai, wajen kula da biyan su hakkokin su da ya dace.

Gwamnan ya ce tuni an kammala shirye-shiryen fara amfani mafin karancin albashi na naira 30,000, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa hannun amincewa.

Ya ce su ma sauran mazauna jihar, gwamnati ba ta bar su a baya ba, musamman wajen ci gaba da gudanar da ayyukan raya jihar a dukkann fadin kananan hukumomin ta 44.

Shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar, Kabiru Ado Minjibir, ya jinjina wa gwamna a kan kokarin nda ya ke yi wajen ganin ya inganta rayuwar ma’aikatan jihar Kano.

Kuma ya yaba da kokarin ganin an fara biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi da gwamnatin jihar Kano a ta fara ba da dadewa ba, kamar yadda gwamnan ya sha alwashi.

Share.

game da Author