Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya bayyana cewa ranar 29 Ga Mayu da kuma ranar 12 Ga Yuni za su rika kasancewa ranakun hutun murnar dimokraiyya.
Don haka y ace daga wadannan ranakun masu zuwa za su kasance ranar rantsar da sabon shugaban kasa da kuma ranar dimokradiyya tun daga wannan shekara.
Jiya Litinin ne Lai ya yi wannan sanarwa a lokacin da ya ke bayyana jerin shirye-shiryen da za a yi na ranar sake rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari.
Lai ya ce daga wannan shekara za a rika yin hutun Ranar Sake Rantsar da Sabon Shugaban Kasa, wato 29 Ga Mayu, sai kuma ranar 12 Yuni za ta kasance tanar murnar dimokradiyya.
Najeriya ta rika hutun ranar dimokradiyya a ranar 29 Ga Mayu, tun bayan komawar kasar a kan mulkin dimokradiyya cikin 2019.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana ranar 12 Ga Juni ta kasance ranar hutun dimokradiyya, biyo bayan amincewar da gwamnatin tarayya ta yi cewa marigayi MKO Abiola ya lashe zaben 12 Ga Yuni, 1993 kuma aka ba shi lambar girma mafi daraja ta GCFR, duk kuwa da cewa ya rasu.
Gaba daya Majalisar Dattawa da ta Tarayya duk sun amince, kuma ranakun duk zama cikin kundin dokar kasa.
Kafin yanzu dai jihohin Kudu Maso Yamma shida ne, yankin da Abiola ya fito, suke yin hutun 12 Ga Yuni, ranar da aka yi zaben shugaban kasa tsakanin Abiola na SDP da kuma Bashir Tofa na NRC.
A wannan shekara kuwa tun daga ranar 7 Ga Yuni za a fara bukukuwan ranar dimokradiyya, inda za a fara bajekolin hotunan tarihi har zuwa ranar 12 Ga Yuni.
Sai kuma ranar Lahadi, 9 Ga Yuni duk dai a Dakin Taro na International Conference Centre, za a yi shagulgunan kade-kade ra raye-raye na yara matasa da dare.
Ranar 10 da 11 ma za a yi wasu tarukan na yara ‘yan sakandare da kuma wani taro kan Shugaba Buhari.
Ranar Laraba, 12 Ga Yuni a yi fareti a Dandalin Eagle Square, sai kuma da dare a yi a yi kasaitaccen shagali a International Conference Centre.
Discussion about this post