RAMADAN: Zamfara za ta raba wa marayu 40,000 kayan abinci da dinkin Sallah

0

Gwamnatin Jihar Zamfara ta kaddamar da shirin raba kayan abincin azumi da na da Sallah ga marayu 40,000.

A wurin kaddamar da rabon kayan, Shugaban Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara, Bashir Sirajo, ya ce an zabo marayu 1,800 daga kowace Masarauta daya a cikin Masarautu 16. Sai Masarautar Gusau aka zabo marayu 3,600.

Ya ce za a raba wa kiwanen su kayan abinci da suka hada da shinkafa, sukari, wake da kuma yadi da kudin dinki.

Dangane da yawan abincin da za a raba kuwa, Sirajo ya ce kowace masarauta za a bai wa wadannan marayu lodin kayan abinci cikin mota biyu da rabi. Sai Gusau za a ba hudu.

A nasa jawabin, Gwamna Abdulaziz Yari ya gargadi jami’an da aka dora wa nauyin rabon kayan abincin su yi adalci, domin amana ce aka damka musu, kayan marayu ne.

Ya kuma yi kira ga jama’a su ci gaba da addu’ar kawo karshen fitinar da Jihar Zamfara ke fama da ita.

A karshen ya ja hankalin mahara da cewa ga babbar dama a lokacin azumi ta samu, wato su gaggauta tuba ga Allah.

Share.

game da Author