Godiya tabbata ga Allah mai Girma da daukaka, Mai kamala a cikin sunayensa, wanda ya siffantu da siffofi na daukaka, Ubangijin sammai da kassai, Na shaida babu abun bauta da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shida abokin tarayya, ma-abucin falala da bata karewa. Na
shaida Annabi Muhammad (SAW) bawansa ne kuma manzonsa ne, Ya Allah ya kara tsira da aminci agareshi da iyalansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka! Bayin Allah, Kuji tsoron Allah, kusani lallai annabinku ya wajabta muku Zakkar Fidda Kai, don ta gyara zuciya kuma ta tsarkake
ta, Allah SWT ya ce “Hakika wanda ya tsarkata (zuciya) ya samu babban rabo” Zakkar Fidda Kai sadaka ce ta wajibi akan kowane Musulmi mai ikon fitarwa.
Ana fitar da Zakkar Fidda Kai ne kafin Sallar Idi, tsarki ne ga mai azumi kuma abinci ne ga talaka, Sahabi Abbadullahi Dan Abbas, Allah ya yarda da shi ya ce, manzon Allah SAW ya wajabta Zakkar Fidda Kai domin tsarkake azumi daga ayyukan da suka tauye shi, kuma domin talakawa su samu abinci, duk wanda ya bayar da ita kafin Idi, to, Zakkar Fidda Kai ne karbabbiya, amma wanda ya bayar da ita bayan Sallar Idi, to, Sadaka ce kamar sauran sadakoki.
An karbo daga Sahabi Abdullahi Dan Umar ya ce, Annabi SAW ya farlanta Zakkar Fidda Kai, SA’I daya (mudun-nibi hudu) akan kowane Musulmi, da ko bawa, mace ko na-miji, babba ko yaro, kuma Annabi SAW ya yi umurni da a fitar da ita kafin Sallar Idi.
Ya ku bayin Allah! Hikimar Zakkar Fidda Kai ita ce sanya farin ciki acikin duk gidajen musulmi ranar Idi, kuma ga samun lada mai yawa, bayyanar da godiyar bawane ga Allah akan ni’imar Azumin Ramadan, kuma Zakkar Fidda Kai tana kusantar da bawa zuwa ga Allah, tana samar dawal-wala da nishadi ga talakawa, kuma tana karesu daga shiga halin kunci da sata don wadatar da iyalansu ranar Sallah. Sabo da haka aka
wajabta ta akan kowa.
Ya ku al’umar musulmi! Wajibcin Zakkar Fidda Kai na tabbata ne akan musulmin da yake da halin fitarwa, ga duk wanda ya mallaki abincinsa na ranar Sallah kuma ya yi rara.
Da zarar rana ta fadi a yinin karshe na ranar Ramadan, to Zakkar Fidda Kai ta wajaba akan kowane musulmi. Wajibin magidanci ne ya fitarwa kansa, da matan sa, da duk wanda yake karkashin kulawar sa, ya nada kyau afitarwa dan da yake jikin mahaifiya sa, miji zai fitarwa
sakakkiyar matar sa idan Iddar ta bata kare ba, wanda ya mutu kafin fitar da Zakkar, to za’a fitar masa a cikin dukiyar sa. Amma Zakkar Fidda Kai tana faduwa akan dukk wanda bai da ikon fitarwa. Allah yana cewa “Baya daurawa rai abinda yafi karfinta”.
Wajibi ne kowane musulmi a fitar masa da SA’I DAYA, wato, MUDUN-NABI hudu, wanada ya yi dai-dai da 3kg. Za’a fitar daga abinci mafi rinjaye a cikin al’uma kuma wanda za’a iya yin abin-cin alfarma da shi, kamar, shikafa, masara, doya, taliya, wake, semobita da sauransu. Yana daga cikin Sunnah a fitar da Zakkar Fidda Kai safiyar ranar Idi kafin Sallar Idi. Kuma ya halatta a fitar da ita kamin ranar Idi da kwana daya ko biyu.
Kuma sahabbai da yawa sukan fitar da ita kamin ranar.
Ya kai mai azumi! Goman karshe na daf da karewa, a cikin wannan wata mai alfarma, goma na rahama, da gafara, da ‘yantawa daga wuta, kasance cikin masu rabo a cikin ciyarwa, ciyarwarka za ta zamo shaida agareka ranar kiyama agaban ubangijin ka, a ranar da za’a baiwa kowa sakamakon aikinsa batare da zalunci ba.
Kar ka zamo cikin marowata, za ka yi asara, bayar da zakar dukiyar ka, kuma kayi sadaka, Allah zai albarkaci dokiyar ka, yaninka maka ninkin-ba-ninkin . Wane ne zai baiwa Allah rance mai kyau? Allah ya nin- ninka masa ninki mai yawa.
Ya Allah kasanya Ramadana ya zamo alkhari da albarka agaremu da sauran musulmi, ka taimake mu a cikin sa da wajen sa cikin dukkan aikin da
zai kusantar da mu zuwa gare ka.
Imam Muhammad Bello Mai-Iyali
Harakatu Falahil Islam
Barnawa Low – Cost
Kaduna – Nigeria