Mazauna yankuna da dama, har da yankin su da Moses Ezakiel ya ke, sun dauki ranar Lahadi da muhimmanci, har ta kai ba su fita zuwa gona noma. Sai dai shi Ezekiel da ya ke tantirin talaka ne, shi da wasu ire-iren sa ba su ga ta zaman gida ranar Lahadi ba.
Ga ranar ana kartsawa mai tsananin zafi a sama da kuma kasa, amma a haka wakilin mu ya hango Ezekiel ya bullo daga cikin duhun bishiyoyi bayan ya yi aiki karcat a gona.
Mutumin mai kimanin shekaru 43 a duniya, ya zauna da wakilin PREMIUM TIMES ya rika bayyana masa irin bakar wahalar da shi da ire-iren sa kananan manoma ke sha a jihar Ogun. Ya kuma rika bada labarin yadda aka yi watsi da su, yadda su ba su ma san irin wani tallafi ko agajin da kananan manoma ke amfana ba, idan ma har akwai agaji ko tallafin.
Ezekiel ya ce a shekarun baya ne dai ake wa noma kirari, har ana ce masa: “Noma yanke talauci.”
Sai ya kara da cewa, “Amma a yanzu mutum zai tafi gona ya yi kartar aiki tun safiya har faduwar rana, hatta ranar Lahadi ma babu fashi. A karshe kuma idan ka tashi sayar da amfanin gonar da ka noma, ba za a saya da daraja ba.”
Ya nuna su dai irin na su noman irin na dawwama a cikin talauci ne, ba na yanke talauci ba ne.
Garin Ilaro da ke cikin Karamar Hukumar Yewa ta Kudu a Jihar Ogun, gari ne da ya fara bunkasa, domin har bankuna akwai da kuma kamfanoni.
Sannan kuma a garin akwai akalla kananan manoma 200 ko sama da haka, banda ma tulin ’yan kwadagon da ke taya su aikin girbi da kwasar amfanin gona zuwa gida.
Sai dai kuma Ezekiel ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa dukkan su dac ke ta hakilon noman a kowace shekara, noman wahala kawai suke yi, saboda sai ka girbe amfanin gonar ka ka na murna, amma idan ka kai kasuwa, ba za a saya da farashi mai daraja da zai iya wanke maka yawan gumin wahalar da ka sha ba.
“Ina kara shaida maka, wannan babbar matsala ta ma fi addabar manoman da ke can cikin kauyuka sosai da ba su cikin garin Ilaro.’’
Ya ce ba a taba kai musu ko kiran su karbi wani tattafin nom aba. Sannan kuma babu wanda ya taba kiran su taron kara wa kananan manoma sanin makamar aikin harkokin noma.
Wani manomi mai suna Baba Funlola, ya kara jaddada cewa gwamnati ba ta san da su ba, kuma gwamnati ta kasa samar da tsarin farashin kayan gona, an bar su suna sayar da amfanin gona a wulakantaccen farashi.
Sai dai kuma daga Ezekiel har Baba Funshola, sun yarda cewa rashin zurfin ilmin da ba su da shi da kuma yadda hukumomin gwamnati suka yi musu nisa, wani karin matsala kuma shi ne ka’idojin da Babban Bankin Tarayya (CBN) ta bijiro da su a kan kananan manoma.
Bugu da kari, wasu manoma masu tarin yawa da PREMIUM TMES ta tattauna da su a yankuna daban-daban a jihar Ogun, sun bayyana cewa, ba su taba gani ko cin moriyar tallafin da ake bai wa manoma ba.
“A baya a kan zo dai wasu su yi mana romon-kunne, su ce mu yi wannan, za a yi mana wancan da sauran su. Daga nan kuma baka kara jin su. Dalili kenan ma duk wanda ya kara zuwa ya yi mana dadin baki, to ba mu daukar sa da muhimmanci.”
NA DAINA NOMA DON SAYARWA, SAI DON CI KAWAI –Egbo
Wata mata mai matsakaitan shekaru, mai suna Ona Egbo, da ke zaune Yewa, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ai tuni ta shafa wa kan ta lafiya, ta daina sayar da amfanin noma da ta yi, saboda haushi da takaici.
Ita ma Nike haka ta furta, ta ce idan ka yi noma ka ce z aka saida, to asara ce kawai, sai dai idan ci za ka yi ne za ka iya maida kudin ka.
“Duk duk yadda ka ke da mai sayen amfanin gonar ka, to cikin wulakanci zai yi maka. Shi kuma idan ya tara amfanin gonar ya kai ya sayar da farashi mai tsada.”
Ta ce idan ba ka goge da iya safara ko kasuwancin amfanin gona ba, to idan ka noma ka sayar, sunan ka wahalle kawai.
Duk dai maganar ta su daya ce, wato rashin karfin jarin yin wadataccen noman da za a iya samun albarkacin damina mai tarin yawa.
KAMAR MANOMAN PAPALANTO KAMAR NA ILARO
Su ma manoman yankin Papalanto cikin Karamar Hukumar Ewekoro, irin kukan su daya da na yankin Ilaro. Watau babbar matsalar su shi ne yadda amfanin gonar da suke yi ba ya da wata daraja a idon masu saye.
Amma sun amince cewa da za a ba su horon sanin makama da sirrin kasuwanci, to za su iya samar wa kayan noman su kasuwa mai daraja.
Wani dattijo da ake kira Baba, manomin tumatir, rogo, masara da sauran amfanin gona a kauyen Elewu-lekan, ya danganta rashin kyakkawan farashin tumatir ya dogara ne a bisa dalilin cewa ba kayan gona da zai iya dadewa bai lalace ba.
“Yanzu ka ga kamar tumatir, su wadanda ke sarin sa daga wurin mu su na kaiwa Sayedero, Lusada, Ayetoro ko Lafinwa su sayar, su na sane da cewa gaggawa mu ke yi mu ga mun sayar musu da tumatir din don kada ya rube ya lalace a hannun mu.”
Ezekiel ya shaida wa wannan jarida cewa a yanzu ana saida buhun rogo naira 1,500 kacal. Wannan farashi kuwa cikin cokali ne idan aka auna irin lokacin da manomi ya bata na aikin gona tun daga shuka, noma dashe har zuwa girbi.