#PHC4UHC:Etsu Nupe ya koka da yadda ‘yan Najeriya ke yawan fita zuwa kasashen waje neman magani

0

Etsu Nupe Yahaya Abubakar ya koka kan yadda ‘yan Najeriya ke yawan fita zuwa kasashen waje domin neman magani a asibitocin su.

Ya ce rashin isassun ma’aikata, rashin ingantattun kayan aiki, rashin ware isassun kudade na daga cikin matsalolin da ya gurguntar da fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Abubakar ya koka da haka ne yayin da tawagar kungiyar NIPPS da DRPC ta kawo masa ziyara a fadarsa dake Bida a jihar Neja ranan Laraba.

” A kullum zaka ji ‘Yan Najeriya na balaguro zuwa kasashen waje domin samun kiwon lafiya mai nagarta saboda namu ya gaza ko kuma ba a iya samun yadda ake so.

” A dalilin me zai sa namu asibitocin ba za su iya samar musu da kiwon lafiyar da suke bukata ba? A gani na idan har muka iya amsa wannan tambaya za mu samu ci gaba a fannin kiwon lafiyar mu.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya wani tsohon ministan kiwon lafiya Onyebuchi Chukwu ya bayyana cewa a duk shekara Najeriya na rasa Naira biliyan 175 a dalilin fita zuwa kasashen waje da mutane ke yi domin samun ingantaccen kula na lafiyar su.

Bayan nan watanni biyu da suka gabata ministan kiwon lafiya Isaac Adewole yace gwamnati na kokarin ta wajen ganin ta inganta fannin kiwon lafiya a kasar nan domin hana hakan ci gaba da aukuwa.

A karshe Abubakar ya ce sarakunan gargajiya na da mahimmiyar rawa da za su taka wajen ganin an inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya a wuraren su.

” Samun nasara wajen yin rigakafi, bada dabarun bada tazarar iyali ya dogara da irin goyan bayan da sarakunan gargajiya za su bada.”

Share.

game da Author