A cikin raha da tsokana, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya gode wa Shugaban Majalisar Dokoki, Bukola Saraki da bai yi amfani da damar da ya ke da ita ya yi wa Shugaba Muhammadu buhari ‘sakiyar dabu ruwa a ranar rantsuwa ba.
Osinbajo ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ake liyafar cin abincin dare jiya Laraba domin karrama Shugaba Muhammadu Buhari da shi Osinbajo, a babban dakin taro na Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
An yi taron bayan Cif Jojin Najeriya, Tanko Muhammad ya rantsar da Buhari da Osinbajo a karo na biyu.
Sai dai Buhari bai samu halarta ba saboda ya na ta shirye-shiryen tafiya Saudiya domin halartar taron Kungiyar Kasashe Musalumi da ake yi a Makkah, Saudi Arabiya.
Osinbajo din ne ya wakilci Buhari a wurin liyafar.
Cikin raha Osinbajo ya ce: “Wato wani wani abu ya faru a dazu cikin dare a kasar nan, wanda ni a matsayi na na lauya kuma malamin shari’a, na fahimci wani al’amari.
“Wato a daidai karfe 12:01 na dazu da dare wa’adin mulkin shugaban kasa ya kare. A dokance babu shugaba da mataimaki kenan.
“Kenan daga wannan lokaci har wayewar gari da safe, 29 Ga Mayu, wajen karfe 10:30, kafin a rantsar da mu, babu Shugaban Kasa da Mataimakin sa a Najeriya.
“Doka ta ce a wannan lokacin Shugaban Majalisar Dattawa ne zai kasance Shugaban Kasa Mai Riko, har zuwa lokacin da za a yi rantsuwa. To abin sha’awa kuma abin murna, babu wani abin da ya faru a wannan tsakani.
“Idan da kun lura, za ku ga a lokacin da na isa filin Eagle Square da safe, za a ga ni da Shugaban Majalisar Dattawa muna raha, mu na tsokanar juna.
“Saraki ce min ya yi ‘to ku fa bi a hankali, saboda ka san dai ni ne Shugaban Kasa na riko a halin yanzu; To don haka mun gode wa Shugaban Majalisa, da bai bi son zuciyar sa ya yi wata makarkashiya ba.” Inji Osinbajo
Daga nan sai ya kara gode wa ’yan Najeriya da suka sake amincewa suka zabe su a karo na biyu.
Ya kuma kara jajjada cewa wannan zango da aka shiga zai zama zangon albarka da yalwar arziki a kasar nan.
A wurin, Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole duk sun yi jawabai.