Najeriya na rasa kwararrun likitoci 2000 dake ficewa zuwa kasashen waje aiki -NMA

0

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA) Francis Faduyile, ya koka cewa ce bincike ya nuna akalla kwararrun likitoci 2000 ne ke ficewa daga kasar nan zuwa kasashen waje a duk shekara.

Faduyile ya koka da haka ne a wata zama da kungiyar ta yi a Abakaliki jihar Ebonyi.

Ya ce hakan na da nasaba ne da rashin kula da jndadin ma’aikatan kiwon lafiya da gwamnatin kasar nan ba su yi.

Faduyile yace dole NMA ta gaggauta daukan matakan da za su taimaka wajen dakatar da haka a kasar nan.

A nashi tsokacin ministan kiwon lafiya Isaac Adewole shima ya koka game da wannan matsalar inda yake tabbatar da cewa gwamnati ta dauki matakan da za su dakatar da haka.

‘‘Gwamnati na iya kokarin ta wajen ganin ta inganta jin dadin ma’aikatan kiwon lafiya a kasar nan sannan ta hada kwawance da kungiyar likitoci ‘yan Najeriya dake aiki a kasashen waje domin yin amfani da kwarewansu wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasan.

Share.

game da Author