Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta fitar da kididdigar cewa a cikin watan Janairu, 2019, mutane 540 ne suka mutu sanadiyyar Hadarin mota a kasar nan.
FRSC ta kuma kara da cewa mutane 3,383 ne suka ji raunuka, sannan kuma sun kididdige yawan hadurra har 940 duk a cikin watan Janairu kadai.
Adadin mutanen da hadarin ya ritsa da su sun kai 7,827, kamar yadda babban jami’an su Boboye Oyeuemi ya sa hannu, kuma ya raba wa manema labarai, jiya Juma’a, a Abuja.
Oyeyemin ya ce yawan wadanda suka mutu a hadarin mota cikin Janairu, duk da sun kai 540, to sun ragu da kashi 21 bisa 100 a kan wadanda suka mutu a cikin watan Disamba.
Haka ma yawan wadanda suka ji ciwo da yawan afkuwar hadarin duk ya ragu da kashi 14 bisa 100 idan aka kwatanta shi dawatan Disamba, 2018.
Kididddigar bayanan FRSC ta nuna cewa titin Lagos zuwa Ibadan ne ya fi samun yawan hadurra a cikin Janairu, har sau 57, watau kashi 11 bisa 100 na hadurran da aka yi gaba daya a Najeriya cikin watan Janairu kenan.
Sai kuma titin Abuja zuwa Lokoja mai yawan hadurra 54 sai Abuja zuwa Kaduna shi kuma hadurra 51, kamar yadda Oyeyemi ya tabbatar.