NAFDAC ta kama jabun kwalaye 401 na abin sha da kuma wadanda wa’adin su ya cika

0

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa (NAFDAC) ta kama kwalaye 401 na abin sha da wa’adin amfanin su ya cika a Minna jihar Neja.

Jami’in hukumar Anikoh Ibrahim ya sanar da haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai.

Ibrahim yace hukumar ta yi nasarar kama wadannan kwalaye bayan an tona asirin wani dan kasuwan dake boye da wadannan kaya a gidan ajiyan kaya da wasu mutane suka yi.

Ya ce gidan ajiyan kayan na bayan kasuwan Gwari dake karamar hukumar Chanchaga ne.

” Mun kama katan 376 na Amstel Malt, katan 17 na Coca-cola da katan takwas na Maltina.

Ibrahim yace bisa dokar hukumar bai kamata ‘yan kasuwa su ci gaba da ajiye kayan abincin da amfanin su ya kare ba.

A kwanakin baya ne Shugaban NAFDAC, Christiana Adeyeye ta yi kira ga mutane da su sa ido sannan su rika tona asirin duk wadanda ke sarrafa jabun magunguna da suka sani ko wani abincin ci ko sha.

Christiana ta ce haka zai taimaka wa hukumar wajen samun nasarar kawar da jabun magunguna daga kasar nan baki daya.

” Yin haka ya zama dole gannin cewa masu sarrafa wadannan magungunan kan yi haka ne cikin dare a wuraren da suke hadawa.”

Daga karshe, ta bayyana cewa idan har jama’a suka hada hannu da ma’aikatan hukumar musamman wajen tona asirin masu sarrafa irin wadannan jabun magunguna za a sami raguwa wajen yawan yaduwar magungunar a kasa Najeriya.

Share.

game da Author