Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shi ba sa’an Sarkin Kano Muhammadu Sanusi bane ko a tsarin dokar kasa.
Ganduje ya ce da shugaban karamar hukuma ya kamata yana sa-in-sa ba gwamna ba domin nan ne hurumin sa sannan daidai shi.
” Gyara ne da ci gaba muka kawo jihar mu. Muna so mu kusanto da mutane kusa da shugabannin su. Amma ba daukar fansa ba ko kuma bibiyar wani.
” Idan ma har zancen ake so a yi ay a karkashin shugaban karamar hukuma ya ke ba gwamna ba.
” Idan ba dun-ba-dun ba, ay da shugaban hukuma ya kamata yake gani idan bukatan haka ya tashi ba gwamna ba domin gwamna ya yi masa nisa. Haka dokar kasa ta gindaya.
” Wannan masarautu da muka kirkiro za mu tabbata mun gyara su sannan mun daga darajarsu da martaba a Idanun mutanen jihar.
Ganduje ya ce mutanen jihar na murna da wannan mataki ya gwamnatin sa ta dauka.