” Na san nauyin dake kaina a matsayina na shugaban kasa kuma na san abinda nake yi” – Inji Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban Najeriya yana sane da irin ayyukan da mutane ke bukata ayi musus kuma ya san abinda yake yi.

Buhari ya fadi haka ne bayan halartar tafsirin Alkur’ani a masallacin fadar shugaban kasa.

Buhari ya ce aikin sa ne ya sa a gaba ” Kuma zamu tabbata mun cika alakwurran da muka dauka wa ‘yan Najeriya.”

Shugaban Buhari dai yana ta shan caccaka daga mutanen Najeriya musamman game da tabarbarewar tsaro a yankin Arewa Maso Yamma.

Idan ba a manta ba Sarkin Katsina ya aika wa shugaba Buhari da sako irin haka inda ya yi kira ga shugaban kasan da ya maida hankali kan matsalar tsaro a jihar Katsina da kasa baki daya domin kawo ayyukan mahara da masu garkuwa.

Sakon Sarkin Katsina ga Buhari

Sarkin Katsina Abdulmumini Usman ya aika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sakon tare da yin kira ga reshi da ya maido hankalinsa matsalar rashin tsaro da ya addabi mutanen jihar da kasa baki daya.

Sarki Kabir ya bayyana haka ne a wajen taron samarwa manoman jihar irin auduga da kayan aikin gona wanda ministan Gona Audu Ogbe da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emiefile suka halarta.

” Ba iri bane ya dame mu yanzu a jihar Katsina, tsaro shine yafi tada mana hankali. Manoma da dama sun arce daga gonakinsu haka suma makiyaya duk sun rasa matsuguni a dalilin ayyukan mahara da masu garkuwa da mutane. Wanna shine ya fi damun mu.

” Kusan kullum sai an kawo mun rahoton ko an kashe wani ko kuma an yi garkuwa da mutane a kauyukan mu. Ina dadi a haka. Ku je ku gaya wa shugaban kasa cewa duk kyawon wadannan shirye-shirye ba za suyi tasiri ba idan babu tsaro. Mu yanzu a gaskiya tsaro shi ya fi damun mu.

” Tsakani da Allah ace wai mahara su shigo har cikin garin Daura su yi garkuwa da babban basarake kamar Magajin Gari. Aiko kasan akwai tashin hankali matuka. Yanzu fa babu wanda yake cikin tsaro, yau ko kana gidan ka ne koko bisa hanya, hankalinka a tashe yake. Haba dai wannan ko wacce irin kasa ce?”

Share.

game da Author