Sabon gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa ya taradda tsohuwar gwamnati ta ciwo bashin har naira biliyan 139.
Bala ya ce duk da cewa akwai matsala matuka a hakan nuni ne cewa dole sai gwamnatin sa ta nemi karin kudade idan har tana so ta cimma burinta ta hanyar ciwo bashi da wasu hanyoyin.
Bala wanda shine ya kada gwamnan jihar Mohammed Abubakar a zaben da ya gabata ya kara da cewa zai maida hankali ne wajen ganin ma’aikatan jihar suna samun albashin su akan kari. Sannan kuma ya ce zai maida hankali wajen biyan kudaden fansho na tsuffin ma’aikata.
Babban jojin jihar Rabi Umar, ce ta rantsar da Sanata Bala da mataimakin sa Sanata Baba Tela.